Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 21:47:45    
An yaye kyallen da ke alamanta bude shiyyar farko ta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Zambiya

cri

Idan an tabo magana kan batun kafa shiyyar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Zambiya da kasar Sin, sai a iya tunawa da taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wanda aka yi a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, a wancan lokaci kuwa, a madadin gwamnatin Sin Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya sanar da cewa, nan da shekaru 3 kasar Sin za ta kafa shiyyoyi 3 zuwa 5 na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a kasashen Afirka, shiyyar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Zambiya da Sin kuwa ta zo ta farko ke nan bisa shirin da aka tsayar. Zuwa shekarar 2010 wato bayan da aka karasa aikin kafa wannan shiyyar, za a shigar da masana'antu 60 na kasar Sin da na kasashen waje cikin shiyyar, kuma za a zuba mata jarin dala miliyan 800, yawan gurabun aikin da za a samar wa mutane ya kai 6000.

Kan batun kafa shiyyar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da zumuncin da ke tsakanin sin da Afirka, Mr. Hu Jintao ya ce, "Zuwana nan Afirka a wannan gami, makasudinsa shi ne domin dankon zumuncin al'ada da ke tsakanin Sin da Afirka, da gudanar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kara hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare."

Lokacin da Mr. Hu Jintao ya tabo magana kan kasar Zambiya ya ce, "Kasar Zambiya wata muhimmiyar kasa ce da ke kudancin Afirka, kuma kasa ce ta farko ta kasashen kudancin Afirak da ta kulla huldar jakadanci da sabuwar kasar Sin. Halin da ake ciki yanzu a kasar Zambiya wajen bunkasa tattalin arziki yana da kyau, muhallin zuba jari kuma yana ta kyautatuwa a kwana a tashi. Kasar Sin ta sa kaimi da nuna goyon baya ga masana'antu masu karfi na kasar da su zuba jari a shiyyar hadin gwiwa don gudanar da ayyukansu, ta yadda za su ba da taimako domin raya tattalin arziki da samun ci gaban zaman al'umman kasar Zambiya."

Mr. Mwanawasa, shugaban kasar Zambiya ya nuna babban yabo ga aikin kafa shiyyar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da aka yi a kasarsa. Ya ce, "Kafuwar shiyyar hadin gwiwa tsakanin Zambiya da Sin wajen tattalin arziki da ciniki ta tabbatar da alkawarin da shugaba Hu Jintao ya dauka a gun taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a shekarar da ta wuce. Jama'ar duk kasar Zambiya baki daya za su samu moriya daga wajen wannan shiyyar, musamman ma za su samu moriya daga wajen gurabun aikin yi da fasaha da samun kyautatuwar kwadago. Bayan kafuwar wannan shiyyar hadin gwiwa, za a kyautata zaman rayuwar jama'a da ke kewayen shiyyar, kuma za a bunkasa tattalin arzikin kasar Zambiya. Muna fatan ganin masana'antu da yawa na kasar Sin za su iya gudanar da ayyukansu cikin shiyyar hadin gwiwa. Zuwansu a nan kuma zai jawo mana damar koyon ilmi da fasaha da fasahar gudanar da harkokin masana'antu, kuma zai kawo mana zarafin bunkasa masana'antun kasar Sin da na sauran kasashe da na kasarmu ta kanmu." (Umaru)


1 2