Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 21:47:45    
An yaye kyallen da ke alamanta bude shiyyar farko ta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Zambiya

cri

A ran 4 ga wata a birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambiya an kafa shiyyar farko ta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da kasar Sin ta kafa a Afirka wato shiyyar hadin gwiwa tsakanin Zambiya da kasar Sin wajen tattalin arziki da ciniki. Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Zambiya da Mr. Levy Mwanawasa, shugaban kasar Zambiya su ne suka yaye kyallen da ke alamanta bude shiyyar tare. To, jama'a masau sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayanin da wakiliyarmu ta musamman ta ruwaito mana daga birnin Lusaka dangane da wannan labari.

Mr. Hu Jintao ya ce, "Shiyyar hadin gwiwa tsakanin Zambiya da kasar Sin wajen tattalin arziki da ciniki ta zama wata shaida ce ta hakika wajen sakamakon taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Kafuwar wannan shiyyar hadin gwiwa ta zama wata babban al'amari ne ga Sin da Zambiya wajen hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, kuma ta ba da shaida cewa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Afirka ya samu bunkasuwa har ya kai wani sabon matsayi".

A gun bikin yaye kyallen shiyyar hadin gwiwa da aka yi a wannan rana kuma, Mr. Hu Jintao ya ce, tun cikin dogon lokacin da ya wuce, bisa ka'idar nuna sahihanci da aminci, da samun moriyar juna cikin halin daidaici, da yin hadin kai da hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare, kasar Sin ta nuna himma da kwazo wajen hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka daga fannoni daban-daban, ta samar wa jama'ar Sin da ta Afirka moriya ta hakika.


1 2