Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-03 18:20:38    
Shugaba Hu Jintao ya ziyarci kamfanin sarrafa man fetur na Khartoum na Sudan

cri

Kasar Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya, kuma nahiyar Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, shugaba Hu ya kara da cewa,'Har kullum gwamnatin Sin na sa kaimi kan masana'antun kasar Sin masu karfi, wadanda su ne yardaddun abokan ciniki da kuma goyon bayansu da su yi hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki ta hanyoyi daban daban a kasashen Afirka da suka hada da Sudan, gwamnatin Sin ta kuma bukace su da su bi ka'idojin moriyar juna da samun bunkasuwa tare, su mai da hankula kan zama yardaddun abokan ciniki da ingancin hadin gwiw, su yi zama mai jituwa tare da mutanen wurin, su dauki nauyin zaman al'umma bisa wuyansu da kansu, sa'an nan kuma su kara yin abubuwan da ke amfana wa karfafa karfin kasashen Afirka a fannin samun ci gaba da kansu, da kuma taimakon jama'ar Afirka wajen kyautata rayuwarsu.' 

Haka zalika kuma a cikin jawabin da ya yi, shugaba Al-Bashir ya yi bayani kan muhimmiyar ma'anar hadin gwiwar man fetur da ke tsakanin kasarsa da Sin, ya ce,'Kasashen Sin da Sudan suna yin hadin gwiwa a fannin man fetur ba domin dalilin siyasa ba, kuma ba a matsa musu lambar siyasa ba, irin wannan hadin gwiwa zai sanya kasashen Afirka da na Larabawa da yawa su mai da hankulansu kan kasar Sin. A gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a shekarar bara, kasar Sin ta gabatar da matakai da ayyuka a jere don goyon bayan bunkasuwar Afirka, ziyarar da shugaba Hu ya kawo wa kasar Sudan a wannan karo za ta bude sabon shafi wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasashen 2, za ta zama sabon mafari ne wajen bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen Sudan da Sin.'

Raya tattalin arziki da kawo wa jama'a alheri da kuma bauta wa al'umma ka'idoji ne kasashen Sin da Sudan ke bi a fannin hada kansu ta fuskar man fetur. A cikin shekaru 10 da suka wuce, Sin da Sudan sun horar da kwararru da yawa daga wajen yin hadin gwiwar man fetur a tsakaninsu, ban da wannan kuma, sun aiwatar da tunanin mayar da tsaron lafiya da kiyaye muhalli da mutane a gaban kome da kuma samun ci gaba cikin jituwa a lokacin da suke yin hadin gwiwar man fetur.(Tasallah)


1 2