Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-03 18:20:38    
Shugaba Hu Jintao ya ziyarci kamfanin sarrafa man fetur na Khartoum na Sudan

cri

Ran 2 ga wata da yamma bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Hu Jintao da ke ziyarar aiki a kasar Sudan ya ziyarci masana'antar sarrafa man fetur na Khartoum, a karkashin rakiyar takwaransa na kasar Sudan Omar Hassan Ahmed Al-Bashir.

A shekara ta 1995, ziyarar da shugaba Al-Bashir ya kai wa kasar Sin ta kaddamar da hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Sudan a fannin man fetur. A watan Maris na shekara ta 1997, kasashen Sin da Sudan sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa, daga nan ne wadannan kasashe 2 sun gama kansu tare wajen raya masana'antun man fetur. A shekara ta 2000, an fara aiki da masana'antar sarrafa man fetur na Khartoum mai jarin kamfanin man fetur da gas na kasar Sin wato CNPC da ma'aikatar makamashi da ma'adinai ta kasar Sudan tare. A shekarar bara kuma, an kammala ayyukan fadada shi, ta haka kasar Sudan ta sami cikakken tsarin masana'antun man fetur na zamani.

Lokacin da yake ziyarar wannan masana'antar sarrafa man fetur, shugaba Hu Jintao ya saurari abubuwan da aka bayar kan wannnan masana'anta a tsanake, ya kuma ba da jawabin cewa,'Kasashen Sin da Sudan sun dauki shekaru 10 suna hada kansu a fannin man fetur. A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, sun sami sakamako da yawa daga wajen hadin gwiwarsu, sun kuma sami riba mai kyau ta fuskar tattalin arziki da zaman al'umma. Hadin gwiwar man fetur a tsakanin Sin da Sudan yana amfana wa ci gaban masana'antun kasar Sin, haka kuma, yana sa kaimi kan kasar Sudan da ta samar da cikakken tsarin masana'antun man fetur, yana kuma ba da gudummowa gare ta wajen yin amfani da albarkatu yadda ya kamata, da samar da guraban aikin yi, da kara samun haraji, da kuma raya tattalin arzikinta bisa gatancin albarkatu. Abubuwan gaskiya sun shaida cewa, hadin gwiwa a tsakanin Sin da Sudan ya zama abin koyi ne a fannin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa.'

1 2