An taba nuna wannan kashin yatsar Sakyamuni mai daraja a Taiwan na kasar Sin, inda masu bin addinin Buddha na wurin suka bauta masa da cikakkiyar zuciya. An mayar da wannan kasaitaccen bikin bautawa da aka yi tun daga ran 23 ga watan Fabrairu zuwa ran 31 ga watan Maris na shekara ta 2002 tamkar muhimmiyar harkar addinin Buddha a ketare mashigin tekun Taiwan. Kashin yatsar Sakyamuni da ake nunawa a gidan ibada na Famensi shi yanki ne kawai na yatsar Sakyamuni a duniya a yanzu, shi ya sa aka mayar da shi a matsayin dukiyar kasar Sin. Ana bauta wa kashin yatsar Sakyamuni tun daga zamanin daular Tang zuwa shekara ta 874, daga baya an rufe shi a cikin wata karamar hasumiya. Masu nazarin kayayyakin tarihi sun tono wannan dukiya a shekara ta 1987, wato bayan shekaru 1113 da aka binne ta a karkashin kasa.
Yanzu za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan', sai ku karkade kunnuwanku domin jin labarin da muke dauke da shi, za mu sake karanta bayanin musamman mai lakabi haka 'gidan Panda, wato gandun daji na Wolong na lardin Sichuan'. 1 2
|