Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-30 22:16:29    
Gidan ibada na Famensi

cri

Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan gidan ibada na Famensi, daga bisani kuma za mu kai ziyara ga gidan Panda, wato gandun daji na Wolong na lardin Sichuan, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan'

Gidan ibada na Famensi wani wuri ne mai tsarki a idanun masu bin addinin Buddha, wanda ke da nisan kilomita 110 daga yammacin birnin Xi'an na lardin Shaanxi na kasar Sin. An gina shi ne a zamanin daular Donghan wato shekara ta 25 zuwa ta 220 bayan haihuwar Annabi Isa Alaihim Salam. Ya shahara ne saboda an ajiye kashin yatsa na Sakyamuni, wanda ya kafa addinin Buddha. Birnin Xi'an ya sami bunkasuwa a zamanin daular Tang, a lokacin nan ya zama birni mafi girma a kasashen gabashin duniya, shi kuma mafari ne na hanyar siliki da aka shimfida a tsakanin Asiya da Turai.

A shekara ta 1987, gidan ibada na Famensi ya jawo hankulan masu nazarin kayayyakin tarihi na duk duniya saboda a lokacin da aka rushe tushen hasumiyarsa don yin mata kwaskwarima, an tono wata fada a karkashin kasa, wadda aka gina ta a zamanin daular Tang. An yi shekaru fiye da 1100 ana binne da rubutun da aka sassaka a kan duwatsu 2 da kuma wasu sauran dukiyoyi a cikin wanann fada, wadanda suka hada da kashin yatsar Sakyamuni.

1 2