Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-30 22:03:35    
Fahimtar al'adu a kan titin shakatawa a Chengdu

cri

 

Saboda wasannin mutum-mutumi na samun karbuwa sosai, shi ya sa malam Zhou Yinong, wanda ya nuna irin wannan wasa a Jinli, ya ji alfahari kwarai. Ya ce,'Mutane da yawa na gida da na waje da ni mun zama abokai. Wani gidan tebilijin na kasar Italiya ya fito da shirye-shirye a wata da ya gabata, inda na koya musu yadda aka yi mutum-mutumin nan da kuma nuna wasanninsu. Sun koya wa mutanensu, ta haka za su fahimci al'adun kasar Sin, na yada al'adun kasar Sin zuwa ketare.'

A duk sallar gargajiya, a kan shirya wasu harkoki masu sigar musamman na al'adun gargajiya a titin Jinli, dukansu kasaitattun bukukuwa ne da ke jawo mazaunan wurin da masu yawon shakatawa da yawa.

Birnin Chengdu ya shahara ne saboda abincinsa mai dadi. Wajibi ne masu yawon shakatawa da suke ziyara a Jinli su dandana wadannan abinci. Mutane na iya cin dukan shahararrun abinci na Sichuan a kan hanyarsu ta ziyarar Jinli, sun kasa rufe bakinsu.

Ban da dakunan shan shayi da dandamali na gargajiya, ya kasance da dakunan shan kofi da giya a kan titin Jinli. Ko da yake wadannan dakunan shan kofi da giya na nuna sigogin zamani, amma sun hada kai da titin Jinli mai sigar gargajiya yadda ya kamata bisa ga kayayyakin gida na gargajiya da rubutu irin na kasar Sin da ke cikinsu, shi ya sa ko kusa ba su kawo illa ga wannan titi ba, sun saje dai dai da wannan tsohon titi.

An raya al'adun wurin na Sichuan da kasuwanci gaba daya a titin Jinli. Tun daga watan Oktoba na shekara ta 2004 da aka kaddamar da shi har zuwa yanzu, titin Jinli da nuna sigogin ala'du na lardin Sichuan sosai wadanda suka jawo dubban masu yawon shakatawa.

To, jama'a masu sauraro, karshen shirinmu na yau na yawon shakatawa ke nan, sai mako na gaba, idan Allah ya kai mu.


1 2