Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-30 22:03:35    
Fahimtar al'adu a kan titin shakatawa a Chengdu

cri

Titin Jinli na kudancin birnin Chengdu, tsawonsa ya kai fiye da mita 350 gaba daya, wanda wani titin shakatawa ne mai salon tsohon gari a birnin Chengdu. Bayan da masu yawon shakatawa suka wuce ta ginshikin da ke jikin kofa, wanda aka rataye jayayen fitilu 2 a kansa, mutane sun sa kafofinsu a kan wani titi, wanda cike yake da sigogin gargajiya. An yi gine-gine ne bisa salon gargajiya a gefunan hanyar, wadda aka yi da duwatsu shudda, kantuna da gine-ginen shan shayi na da benaye 2 ko 3 kawai, tubala masu launin toka-toka na bango da kuma ginshikai masu launukan ja da baki na hanyoyin cikin gida sun nuna sigogin gargajiya. Kantunan da ke sayarwa da kayayyakin gargajiya sun sami rinjaye a kan wannan titi, inda ake nuna fadi-ka-mutu da kayayyaki iri daban daban da aka yi da hannu, mutane na nuna sha'awa sosai a kansu, har sun manta da komawa. Malam Yang Ming, wanda ya zo daga lardin Taiwan na kasar Sin, ya bayyana cewa, 'Ina jin farin ciki saboda yin yawon shakatawa a titin Jinli, wanda cike yake da sigogin gargajiya. Ana sayar da kayayyakin gargajiya da abinci masu dadin ci da yawa a nan, abincin da ake samarwa a Chengdu na da dandano sosai.'

Titin Jinli yana fitowa da kyakkyawan yanayin al'adu. Abubuwan fasaha da masu sana'ar hannu suke sayarwa a kan titin sun fi jawo hankulan mutane, su kan tunatar da su kyakkyawar rayuwar yarantaka domin ganin wadannan abubuwan da su kan yi wasa da su a lokacin da suke kanana.

Akwai wani fili a tsakiyar titin Jinli, inda aka gina wani dandamalin gargajiya. A kan nuna wasannin gargajiya irin na Sichuan a cikin lokaci kamar yadda aka tsara a kan wannan dandamali mai dogon tarihi. Amma masu yawon shakatawa sun fi son kallon wasannin mutum-mutumi irin na Jinli. Wasannin mutum-mutumi fasaha ce ta gargajiya ta kasar Sin, yau sama da shekaru dubu daya da aka fara yinsu. Bayan da masu sana'ar hannu suka yanka fata da alkamashi, suka kuma yi musu ado a tsanake, bayanannun kananan mutum-mutumi da aka yi da fata sun nuna tarihi. A ko wace rana mutane su kan yi cunkuso a kewayen wuraren da aka nuna wasannin mutum-mutumi a Jinli, musamman ma wadanda suka zo daga kasashen waje, sun fi nuna sha'awa a kan wadannan wasanni. Ga shi, 'Ni ce Catherine, ni ne Roy. Dukanmu mun zo daga kasar Australia, mun yi minti 10 muna tsaye a kan wannan titi, amma a gaskiya kuma muna son yanayin nan. Jajayen fitilun da aka rataya a dukan titin na da kyan gani, sun dumama mu sosai, mun fi son kallon wasannin mutum-mutumi, Lale,wannan wani abu ne mai ban sha'awa kwarai a gare mu.'

1 2