Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-25 16:57:59    
Kulla zumunci da kuma taimakawa juna don samun ci gaba tare

cri
 

A watan Nuwamba na shekarar 2006, a gun bikin budewar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da aka shriya a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya shelanta cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta tura samari masu aikin sa kai da yawansu ya kai 300 zuwa kasashen Afrika. Tura samari masu aikin sa kai na rukunin nan na kasar Sin zuwa birnin Harare shi ne karo na farko da kasar Sin ta yi don bauta wa kasar Zimbabuwei bayan taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika . Matsaikatan shekarun haihuwa na kowane mai sa kai ya kai 29, daga cikinsu da akwai wani Dokta, tare da wadanda suka sami digiri biyu guda 6 da sauransu, za su yi aikin sa kai a kasar Zimbabuwei wajen kiwon dabbobi da tsire-tsire da gyara amfanin gona da koyar da harshen Sinanci da koyar da ilmin Kunputer da ba da ilmin motsa jiki da likitanci da sauransu.

A gun bikin maraba, ministan bunkasuwar samari da samar da aikin yi na kasar Zimbabuwei Ambrose Mutinhiri ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Zimbabuwei ta yi maraba da zuwan samari masu aikin sa kai na kasar Sin a kasarta , gwamnatin Zimbabuwei ta nuna goyon baya ga samari masu sa kai na kasar Sin ta hanyar hukumomin ba da hidima daban daban ta yadda za su yi ayyukansu lami lafiya. Jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Zimbabuwei Yuan Nansheng shi ma ya bayyana fatansa ga samari masu aikin sa kai na kasar Sin , ya ce, kasar Sin da kasar Zimbabuwei suna da zumuncin gargajiya mai danko sosai a tsakaninsu, kullum kasar Sin tana maida da kasar Zimbabuwei bisa matsayin abokiya mai amincewa, kuma gwamnatin kasar Sin tana samar wa gwamnatin Zimbabuwei da jama'arta taimakon da ta iya samarwa, gwamnatin kasar Sin ta amince cewa, samari masu aikin sa kai na kasar Sin da suka sauka kasar zimbabuwei tabbas ne za su iya ba da gudumuwarsu ga kasar Zimbabuwei a fannoni daban daban.(Halima)


1 2