A ranar 24 ga wannan wata, a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabuwei, an shirya wani gaggarumin biki don maraba da wasu bakin musamman wadanda su ne samari masu aikin sa kai da suka zo daga kasar Sin. A cikin shekara daya mai zuwa, wadannan samari masu aikin sa kai na kasar Sin za su yi ayyukan sa kai wajen kiwon dabbobi da sha'anin noma da ba da ilmi da likitanci da dai sauransu.
A cikin amon gangar Afrika da ke cike da farin ciki da aminci sosai, samari masu aikin sa kai 15 wadanda suka sanya tsabtaccen kwat mai launin baki sun tsaya a cibiyar taron da aka shriya, dukansu sun lika baje irin na samari masu aikin sa kai na kasar Sin a kirjinsu, a cikinsu da akwai wani saurayin da ya jawo hankulan mutane sosai, sunansa shi ne Xu Benyu wanda ya zo daga shiyyar manyan tsaunuka da ke yammacin kasar Sin, ya zo nahiyar Afrika ne don ba da ilmi dangane da harshen Sinanci, ya bayyana cewa, a shekarar 2002, na yi niyyar zama malamin koyarwa a kasashen waje, kodayake na taba aikin sa kai a lardin Guizhou na kasar Sin, kuma ba na son rabuwa da yaran da suke zama a wurin, amma kowane mutum yana da nasa buri, a ganina, ya kamata ya cim ma burinsa a lokacin da ya ke cike da kuzari sosai, yanzu, ina aikin koyar da harshen Sinanci a wata jami'ar Harare tare da wani mai sa kai na kasar Sin daban, zan yi kokari sosai don yin aikin da kyau.
1 2
|