Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-23 18:27:39    
Taron dandalin tattalin arzikin duniya zai kara haifar da fahimtar tattalin arzikin duniya

cri

Taron da za a yi a wannan shekara yana da jigogi hudu, wato su ne tattalin arziki da siyasar kasa da kasa da fasaha da zaman al'umma da kuma masana'antu. A ganin jami'an dandalin, tattalin arzikin duniya na bukatar sabon kaimi da kuma jagoranci. A matsayinta na rukunin tattalin arziki mafi girma, rashin daidaituwar bunkasuwar tattalin arzikin Amurka kuma babban gibin kudinta sun jawo wa jama'a damuwar ko tattalin arzikin Amurka na iya ci gaba da karuwa, a sa'i daya kuma, sakamakon hauhawar darajar kudin Euro, yawan kayayyakin da ake fitarwa daga yankunan da ke amfani da kudin Euro ya ragu, kuma tasirin da yake kawo wa tattalin arziki ma ya fara tasowa. Ban da wannan, dandalin yana kuma ganin cewa, yankin gabas ta tsakiya, musamman ma tashin hankalin da ake samu a Iraki, da hadarin yaduwar manyan makaman kare dangi da tsarin makamashi na duniya da sauye-sauyen yanayi, dukansu suna da nasaba sosai da tattalin arziki, kuma suna kawo wa tattalin arzikin duniya barazana da kalubale, haka kuma sun yi nuni da cewa, siyasar duniya na bukatar sabon jagoranci. Sa'an nan, sakamakon saurin bunkasuwar fasahohin giza-gizan sadarwa na internet, kowa na iya samun labaran waje, wadannan sabbin sauye-sauye za su kawo babban tasiri a kan tsarin kula da masana'antu da kuma tsarin gudanar da harkokin kasuwanci.

An ce, a lokacin taron, za a shirya tarurrukan nazari na musamman sama da 200, wadanda ke shafar fannoni daban daban na tattalin arziki da zaman al'umma, kuma halin da gabas ta tsakiya ke ciki da shawarwarin zagayen Doha da dumamar yanayin duniya za su kasance muhimman jigogi uku daga cikinsu. An ce, manyan kusoshin gabas ta tsakiya, ciki har da shugaban hukumar Palasdinu, Mr.Mahmud Abbas, da sarkin kasar Jordan Abdullah ?, da firaministan kasar Lebanon Fouad Siniora da mataimakin firaministan Isra'ila Shimon Peres da ministan harkokin waje na kasar, Tzipi Livni za su halarci taron, kuma za su yi taron asiri don neman fid da gabas ta tsakiya daga mawuyacin halin da yake ciki. Ban da wannan, ana kuma daukar shawarar da Mr.Pascal Lami, babban darektan WTO ya gabatar dangane da shirya karamin taron ministoci a lokacin taron, a matsayin wani yunkuri na neman maido da shawarwarin zagayen Doha.

Ban da wannan, shugabanni da kusoshin gwamnati sama da 20 su ma za su halarci wannan taro, ciki har da firaministan kasar Birtaniya, Tony Blair, firaministar kasar Jamus, Madam Angela Merkel, da shugabannin kasashen Mexico da Afirka ta kudu da Brazil da dai sauransu. Shugabannin dai za su bayyana ra'ayoyinsu kan siyasa da tattalin arzikin duniya da dai sauran muhimman batutuwa a lokacin taron.(Lubabatu)


1 2