Daga gobe ranar 24 zuwa ranar 28 ga wata, za a kira taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya a karo na 37 a birnin Davos na kasar Switzerland, kuma shugabannin siyasa da kusoshin bangaren tattalin arziki da yawansu ya zarce 2400 wadanda suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 90 za su bi wannan jigo su tattauna sabbin sauye-sauyen da aka samu daga fannin tattalin arzikin duniya, don neman hanyoyin daidaita matsalolin da abin ya shafa.
Taron shekara shekara na Davos na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya wani muhimmin dandali ne na yin mu'amala tsakanin bangarorin tattalin arzikin duniya, wanda har ake kiransa babban taron tattalin arzikin duniya da ba na gwamnati ba. A kan saka wa ko wane taron shekara shekara wani jigo, don bayyana siga mafi muhimmanci na tattalin arzikin duniya.
1 2
|