Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-19 10:40:22    
Kasashen duniya na kokarin zaunar da gindin Somaliya

cri

A nasa bangaren, Mr. Yusuf ya fadi ,cewa yanzu gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya tana yin shawarwari tare da shugabannin kungiyoyi da na rukunoni daban daban, inda suka rigaya suka samu dan ci gaba kadan. A sa'I daya kuma, ya yi fatan Mr. Fall da kuma ofishin kula da harkokin Somaliya na Majalisar Dinkin Duniya za su yi kaura zuwa birnin Mogadishu.

A ran 18 ga watan da muke ciki, kungiyar tarayyar Arika ita ma ta bayar da wata sanarwa cewa, majalisar zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kungiyar za ta yi zamanta a ran 19 ga wata don zakulo sabon rahoton da aka gabatar a game da halin da ake ciki yanzu a kasar Somaliya da kuma tattauna maganar tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa wannan kasa. Kafin wannan lokaci, kasashen Libya da Habasha su ma sun bayyana aniyarsu ta tallafa wa kasar Somaliya; Bugu da kari kuma, kungiyar IGAD wato kungiyar raya gwamanatocin kasashen gabashin Afrika da kungiyar tarayyar Larabawa da dai sauran kungiyoyi na kasa da kasa da na shiya-shiyya su ma suna yin kokari matuka ta hanyar diplomasiyya wajen zaunar da gindin kasar Somaliya.

Jama'a masu saurare, abun da ya fi jawo hankulan kasashen duniya a halin yanzu, shi ne maganar tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa Somaliya don kiyaye odar al'ummar kasar nan. Firaminista Ali Mohamed Ghedi na gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ya ce, za a girke sojoji masu kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika da suka hada da na kasashen Afrika ta Kudu, da Nigeria, da Malawi, da Uganda da kuma Tanzania da dai sauransu a kasar Somaliya nan da makonni biyu masu zuwa.

Wasu manazarta a fannin diplomasiyya sun yi hasashen cewa, ya kamata gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ta kara yin kokari wajen zaunar da gindin kasar da kuma inganta aikin sulhuntawa tsakanin kabilun kasar yayin da kasashen duniya suke bada taimakonsu. ( Sani Wang )


1 2