Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-19 10:40:22    
Kasashen duniya na kokarin zaunar da gindin Somaliya

cri

Mr. Francois Lonseny Fall, wakilin musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da maganar Somaliya, jiya Alhamis ya isa birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somaliya domin yin shawarwari tare da shugaba Abdullahi Yusuf na kasar Somaliya a game da hallin da ake ciki yanzu a kasar. Ban da wannan kuma, a wannan rana, kungiyar tarayyar Afrika ta yi shelar gudnar da wani taron musamman a yau Jumma'a domin tattauna maganar tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somaliya. Duk wadannan dai sun shaida, cewa kasashen duniya suna namijin kokari wajen zaunar da gindin kasar Somaliya.

Mr. Falla ya yi hasashen cewa, bisa matsayin wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin Somaliya, labuddah ganawar da za a yi tsakaninsa da shugaba Yusuf tana da muhimmancin gaske. Bisa dalilin tsaro ne, aka kafa ofishin kula da harkokin Somaliya na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya dake makwabtaka da Somaliya.

Dawainiya ta farko dake gaban gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya bayan da ta fatattaki 'yan bindiga na mazhaba da kuma kwato ikon akasarin yankunan duk kasa baki daya, ita ce zaunar da gindin kasar da kuma ingiza yunkurin sulhuntawa tsakanin kabilun kasar. Game da wannan dai, Mr. Fall ya bayyana ra'ayinsa, cewa yanzu lokaci ne mafi kyau na kawo karshen halin kara-zube da ake ciki a kasar Somaliya har na tsawon shekaru 16. ya kuma ce, kasashen duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya suna begen ganin wata kasar Somaliya mai jituwa. Daga baya, Mr. Fall ya yi kira ga shugabannin gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya da su tuntubi mutane na bangarori daban daban don neman kafa wata gwamnatin da za ta hada da dukan kungiyoyi da rukunoni; Dadin dadawa, Mr. Fall ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Somaliya da su yi hakuri da juna da kuma kawar da kyamar da suka yi tsakaninsu don ba da taimako ga sake raya kasar. A karshe dai, Mr. Fall ya yi fatan kungiyar tarayyar Afrika za ta tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somaliya ba tare da bata lokaci ba don cike guraben sojojin kasar Habasha bayan da suka janye jikinsu daga wannan kasa.

1 2