Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-05 21:01:15    
Kasar Sin da kungiyar ASEAN sun shiga kyakkyawan lokacin hadin kai a fannin tattalin arziki da cinikayya

cri

A cikin shekaru 15 da suka wuce, kasashen kungiyar ASEAN sun riga sun zama daga cikin kasashe da kasar Sin ke jawo kudin jari daga kasashen waje. Sa'an nan kuma su ne kasashe da masana'antun kasar Sin ke sha'awar zuba musu jari ainun. Ya zuwa karshen shekarar 2005, yawan kudin jari da kasashen kungiyar ASEAN suka zuba a kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 38.5, haka nan kuma yawan masana'antu da aka kafa bisa jarin kasar Sin ya wuce 1000 a kasashe 10 na kungiyar ASEAN.

Madam Duyoanh, jami'ar zartaswa ta cibiyar sa kaimi ga zuba jari da cinikayya ta birnin Ho Chi Minh na kasar Vietnam ta bayyana cewa, "mun kafa cibiyar musamman ta sa kaimi ga zuba jari da cinikayya, domin bauta wa masana'antu masu zuba jari a fannin labaru da manufofi da sauransu. Muna kyakkyawar maraba da zuba jari a fannin ba da ilmi da kasuwanci da sauransu."

Bikin baje koli da Sin da kungiyar ASEAN su kan shirya cikin hadin guiwarsa sau daya a ko wace shekara, wata hanya ce mai muhimmanci ga ingaza zuba jari a tsakanin bangarorin biyu. Malam Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin wanda ya halarci bikin baje kolin da aka shirya a shekarar nan ya bayyana cewa, "a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an sami ci gaba da sauri sosai wajen bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, yawan kudi da ake samu daga wajen cinikayya zai karu da sama da kashi 20 cikin dari a bana. Zuwa shekarar 2010, yawan kudin cinikayya da za a samu a tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN zai kai dalar Amurka biliyan 200." (Halilu)


1 2