Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-05 21:01:15    
Kasar Sin da kungiyar ASEAN sun shiga kyakkyawan lokacin hadin kai a fannin tattalin arziki da cinikayya

cri

Shekarar nan zagayowar shekara ta 15 ce da aka kulla huldar tattaunawa a tsakanin Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN. A kwanakin baya ba da dadewa ba, shugabannin kasar Sin da na kasashen kungiyar ASEAN guda 10 sun taru a birnin Nanning, fadar gwamnatin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, sun tsara babban kasafi mai kyau na samun bunkasuwa a nan gaba. Bangarorin nan biyu sun dau niyyar kammala aikin kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN daidai lokacin da aka tsara wato shekarar 2010.

Yau da shekaru 15 da suka wuce, an fara yin tattaunawa a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, wato ke nan an bude wani sabon shafi ga hulda da ke tsakaninsu. A sakamakon kyautatuwar tsarin hanyoyin zirga-zirga da raguwar harajin kwastan, yawan kudi da bangarorin biyu suka samu daga wajen cinikayyar kayayyaki ya karu da ninki 15 a cikin shekaru 15 da suka wuce, yanzu, kungiyar ASEAN ta riga ta zama abokiyar cinikayya mafi girma ta hudu ga kasar Sin.

A gun taron koli da aka yi a birnin Nanning na kasar Sin a karshen watan Oktoba da ya wuce don tunawa da ranar cika shekaru 15 da kulla huldar tattaunawa a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, Madam Gloria Macapagal Arroyo, shugabar kasar Philippines, wadda ke shugabancin kungiyar ASEAN a yanzu ta bayyana cewa, kungiyar ASEAN da Sin za su zurfafa huldarsu ta hanyar kafa yankin cinikayya cikin 'yanci. Ta ce, "muna ta bunkasa harkokin cinikayya a tsakaninmu da kasar Sin, kuma muna fatan kasar Sin za ta kara zuba kudin jari mai yawa a kasashen kungiyar ASEAN. Yanzu, kasar Sin ta riga ta tashi tsaye a duniya, haka kuma kungiyar ASEAN. Wadannan manyan sauye-sauye ne. Shugabannin kasashe daban daban suna kyakkyawar maraba da zurfafa hulda a tsakanin bangarorin biyu ta hanyar kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a tsakaninsu."

1 2