Bisa matsayinta na mai sana'ar musamman, madam Magret Chan tana da fasahohi da yawa wajen aikin kiwon lafiyar jama'a, ta fahimci dokokin ayyukan kungiyar WHO sosai, kuma ta tsara tsararren shirin da za ta yi a nan gaba domin wannan kungiya. Amma yanzu ana fuskantar barazanar kiwon lafiya a wasu bangarori ko kuma a duk duniya baki daya, aikin da madam Magret Chan za ta dauka yana da nauyi a bayyane. Mr. Liu Jun, wani shahararen mamemi labaru na jaridar "Guangmingribao" ta kasar Sin da ke birnin Geneva ya taba neman labaru daga wajen madam Magret Chan har sau da yawa, kuma ya kallaci yadda madam ta bullo karo na farko cikin kungiyar WHO bayan da ta zama shugabar hukumar kiwon lafiya ta Hongkong, ya bayyana cewa, "Ana iya cewa, madam Magret Chan ta ci zaben zama babbar jami'ar kungiyar WHO ne a lokacin da ake gamuwa da hadari. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, muna iya gane cewa, ba a kawar da tsoffin cututtuka masu yaduwa kwata-kwata ba, sai sabbin cututtuka masu yaduwa sun bullo kuma sun fi na tsoffi mugunta. Daidai sabili da wadannan cututtuka na sabon salo wadanda aka same su ba bisa doka ba, shi ya sa sun jawo kalubale ga kungiyar WHO sosai".
Bisa matsayin 'yar takara wajen zabe da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, a lokacin da ake yin yakin neman zabe, madam Magret Chan ta samu babban goyon baya daga wajen gwamnatin tsakiya da ta yankin musamman na Hongkong na kasar Sin. Ta ci zaben zama babbar jami'ar kungiyar WHO, wannan ya jawo hankulan duk kasashen duniya baki daya, kuma ya zama muhimmiyar alamar kara karfin Asiya cikin kungiyoyin kasashen duniya.(Umaru) 1 2
|