Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-04 14:29:44    
Madam Magret Chan ta hau kujerar babbar jami'ar kungiyar WHO

cri

Ran 4 ga watan Janairu rana ce ta sha bamban da sauran ranaku ga madam Magret Chen, sabo da a wannna rana ta fara gudanar da aikinta bisa matsayin babbar jami'ar kungiyar WHO wato kungiyar kiwon lafiya ta duniya. Bisa wannan sabon matsayin da ta samu, ta yaya za ta ba da taimakonta ga kungiyar a nan gaba? To, jama'a masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana daga birnin Geneva wanda yake da lakabi haka, Madam Magret Chan ta hau kujerar babbar jami'ar kungiyar WHO.

Bayan da madam Magret Chan ta ci zaben zama babbar jami'ar kungiyar WHO, ta bayyana da zuciyarta cewa, "Ba shakka kungiyar WHO za ta ba da taimako ga daidaita matsalolin kiwon lafiya da suka shafi dukkan shiyyoyi da kasashe da kuma jama'arsu, amma ya kamata da farko mu taimaki kasashe da jama'a wadanda suka fi bukatar samun taimako."

Kan manyan ayyukan da ke gaban ta, madam Magret Chan ta kasu wadannan ayyuka kashi 6, kuma ta tsai da muhimman abubuwa 2, wato matsalar kiwon lafiyar jama'ar Afirka da ta matan duk duniya baki daya. Ta ce, "Abun musamman da ya kamata na jaddada a kai shi ne, ya kamata a yi amfani da karfin kungiyar WHO da na kasashen duniya domin daidaita matsalar kiwon lafiyar jama'ar Afirka da ta matan duk duniya. Jama'ar kasashen Afirka da matan kasashe masu fama da talauci suna shan wahala kwarai sabo da cututtuka masu tsanani, ba za a iya jurewa irin wannan halin da ake ciki ba, dole ne a kyautata shi."

1 2