Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-02 18:47:46    
Tabkin Yansaihu

cri

Assalamu alaikun. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan tabkin Yansaihu, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, ziyarar kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong ya yi kamar yadda kai ziyara ga Aljannar da ke duniyarmu, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan'.(music)

Tabkin Yansaihu na cikin lardin Hebei na kasar Sin, wanda wani babban wurin shatakawa ne da ke kusa da shahararriyar Babbar Ganuwa ta kasar Sin. Yana da nisan misalin kilomita 9 a tsakaninsa da Matsatsar Shanhaiguan wadda ake kiran matsatsa ta farko ta Babbar Ganuwa ta kasar Sin. Tsawonsa ya kai misalin kilomita 15, kuma zurfinsa ya wuce mita 60, ya kuma yi wa kansa hanyar ruwa mai kwane kwane a tsakanin tsaunuka 2.

A cikin kananan jiragen ruwa ne masu yawon shakatawa suke iya jin dadin ganin dogayen hayi da ke tsayawa a gefunan tabkin. Ruwan tabkin na da tsabta sosai , ya yi kamar wani madubi, wanda yake bayyana bishiyoyi kwarra da ke rufe tsaunuka. A lokacin da suke tukin jiragen ruwa a wannan tabki, tabbas ne masu yawon shakatawa su kan ji kamar yadda suke a kogin Lijiang na Guilin ko kuma Sanxia na kogin Yangtze.

1  2