Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-02 18:05:07    
Kasar Sin ta yi kwaskwarima kan "Dokar Kiyaye Yara"

cri

Tabbatar wa yara kwanciyar hankali yana daya daga cikin batutuwan da suka fi jawo hankulan iyaye. Bisa ka'idojin da aka tsara a cikin wannan sabuwar dokar kiyaye yara, lokacin da ake ta da hadari mai tsanani a masana'antu ko a wuraren jama'a, dole ne a sanya aikin kiyaye yara a gaban kome. Wato, dole ne a bi ka'idojin "ikon yara ya fi kome muhimmanci" da yawancin kasashen duniya suke bi lokacin da aukuwar hadari.

Daliban kasar Sin suna da babban nauyin karatu da aka dora musu. Wannan wata babbar damuwa ce da yara na kasar Sin suke ji. Iyaye da malamai masu dimbin yawa su kan nemi dalibai da su rage tsawon lokacin yin wasa da na hutu da na yin motsa jiki da su kara yin kokarin karatu domin neman wani kyakkyawan sakamako na karatu. Amma, tun daga yanzu, idan iyaye da makarantu su ci gaba da yin haka, za su karya dokar. Mr. Yu Jianwei, wani jami'in kwamitin kula da harkokin cikin gida da na shari'a na zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Game da nauyin karatu da ake dora wa dalibai, a cikin wannan sabuwar doka, an tsara ka'idojin cewa, dole ne iyaye da makarantu su yi hadin guiwa su tabbatar wa dalibai isassun lokutan yin hutu da wasa da motsa jiki. An hana su da su kara wa dalibai nauyin yin karatu. Amma wannan batu ne mai sarkakkiya. Dole ne a yi gyare-gyare kan tsarin jarrabawa kwata kwata."

A cikin wannan doka, an nemi gwamnatin kasar Sin da ta kara mai da hankali kan aikin kiyaye yara. Bisa wannan sabuwar doka, dole ne gwamnatin kasar Sin ta sanya aikin kiyaye yara a cikin tsarin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma na duk kasar. Kuma za a kafa hukumomin ba da taimakon jin kai da kiyaye yara masu bugiya. A ran 1 ga watan Yuni na shekarar 2007 ce za a soma aiwatar da wannan Dokar Kiyaye Yara. Lokacin da yake tabo amfanin wannan doka, Mr. Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamiti na majalisar dokokin kasar Sin ya ce, "Yara manya gobe. Game da matsaloli masu tsanani da ake fuskantar da su lokacin da ake yin aikin kiyaye yara, zaunannen kwamiti na majalisar dokokin kasar Sin ya yi kwaskwarima kan 'Dokar Kiyaye Yara' gaba daya. A cikin wannan sabuwar doka, an kara jaddada nauyin kiyaye yara da ke wuyan iyaye da makaranta da zaman al'umma har da duk kasar. Tabbas ne wannan sabuwar doka za ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye hankali da halaltattun iko na yara domin yara za su iya yin girma lami lafiya." (Sanusi Chen)


1  2