Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-02 18:05:07    
Kasar Sin ta yi kwaskwarima kan "Dokar Kiyaye Yara"

cri

Kwanan baya, an kammala aikin yin gyare-gyare kan "Dokar Kiyaye Yara" a kasar Sin. A cikin wannan sabuwar doka, an yi gyare-gyare a jere, alal misali, za a hana yara da su shiga dakunan internet,bai kamata makarantu da iyayensu su kara wa yara ayyukan gida na karatu ba da dai makamatansu. A cikin wannan doka, ana kokarin kafa wani kyakkyawan muhalli ga yara lokacin da suke girma da kuma yin watsi da damuwar da suke ji.

A shekarar 1992 ce aka soma aiwatar da "Dokar Kiyaye Yara" a kasar Sin. An taba bayyana cewa, wannan doka karamin tsarin mulki ne ga yara wajen yunkurin kiyaye su. Amma, a cikin wadannan shekeru fiye da 10 da suka wuce, kasar Sin ta samu sauye-sauye sosai a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma. Kasar Sin ta gamu da wasu sabbin matsaloli kan yadda za a kara kiyaye yara a cikin sabon halin da muke ciki yanzu. Dalilin da ya sa aka yi gyare-gyare kan wannan doka shi ne, daidaita wadannan matsalolin da suke kasancewa a gabanmu. Mr. Zhu Mingshan, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin cikin gida da na shari'a na zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin ya bayyana cewa, "Ba mu da cikakken tsarin kiyaye yara. Iyaye ba su cimma ko ba su iya cimma nauyin kiyaye da sa ido kan yara yadda ya kamata ba. A waje daya kuma, ya kasance da matsalolin rashin kwanciyar hankali a cikin makarantu. Sa'an nan kuma, ya kasance da batutuwa game da yadda za a iya samar da taimakon jin kai ga yara masu bugiya da almajirai yara da dai sauransu. Bugu da kari kuma, yaya za a iya kyautata muhallin zaman al'umma ga yara lokacin da suke girma da yin rigakafi da rage aukuwar laifuffukan da yara suke yi, sun zama muhimman batutuwan da ake kokarin daidaita a cikin wannan sabuwar dokar kiyaye yara."

1  2