A cikin irin wannan hali ne, yankin tatalin arzikin nan yake dora muhimmanci sosai ga aiwatar da wasu ayyuka da ya zaba bisa matsayinsa mai rinjaye. Alal misali. Birnin Fangcheng tashar jiragen ruwa ne da ke a ni'imatacen bakin mashigin teku na Bac Bo. Yanzu, an riga an gina wannan tashar jiragen ruwa da ya zama daya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa guda 9 a kasar Sin. Malam Ren Weibin, shugaban ofishin babban kamfanin gudanar da harkokin tashar jiragen ruwa ta Fangcheng ya bayyana cewa, "tashar jiragen ruwa ta Fangcheng tana da matsayan jiragen ruwa guda 35, daga cikinsu akwai manyan matsayan jiragen ruwa guda 21 inda jirgin ruwa mai nauyin ton dubu 10 ke iya zamewa. Yanzu, ana amfani da tashar nan wajen jigilar kayayyaki a tsakanin wurare da ke kudu maso yammacin kasar Sin da wurare da ke kudu maso tsakiyar kasar. Kuma ta bude hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa masu daukar kwantena a tsakaninta da tashoshin jiragen ruwa guda 220 na kasashe da shiyyoyi sama da 70. "
Yanzu, jihar Guangxi ta kasar Sin tana kokari sosai wajen raya yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo da ya zama sansanin cinikayya da kasuwanci da sufuri a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, da sansanin kere-kere da cibiyar musanyar labaru. Jihar Guangxi za ta zama wata sabuwar jiha mai haske yayin da ake bunkasa tattalin arzikin yammacin kasar Sin. (Halilu) 1 2
|