Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-22 20:31:34    
Yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo na jihar Guangxi a yammacin kasar Sin

cri

Jihar Guangxi tana daya daga cikin jihohi 12 da ke a yammacin kasar Sin. A watan Yuli da ya wuce, gwamnatin jihar ta gabatar da shirin kafa yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo, don gaggauta bunkasa harkokin tattalin arzikinta. Malam Wang Naxue, mataimakin shugaban ofishin hukumar kula da harkokin kafa yankin tattalin arzikin nan ya bayyana cewa, "yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo wani bakon abu ne. Abin da ake nufi da shi, shi ne yankin tattalin arziki ne da ke hade da biranen "Beihai" da "Qinzhou" da "Fangcheng" da wurare da ke karkashin mulkin birnin Nanning, fadar gwamnatin jihar Guangxi. Duk duk fadinsa ya kai murabba'in kilomita 42500, yawan mutanensa kuma ya kai miliyan 12.2. "

Me ya sa aka tsara shirin mayar da wadannan birane hudu da su zama yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo na jihar Guangxi? Malam Wang Naxue ya amsa cewa, "dalilin da ya sa haka shi ne domin yankin nan na da matukar muhimmaci ga manyan tsare-tsare, yankin yanki ne mai albarkar ma'adinai, yana da kyakkyawar makomar samun bunkasuwa. Ya yi iyaka da kasashe daban daban da ke cikin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN ta kasa da teku. Ya zama gada da mahada a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN. Ka zalika tsawon bakin teku na jihar Guangxi ya kai kilomita 1600. Teku albarkatu ne masu matukar muhimmanci ga aikin bunkasa harkokin tattalin arziki na zamani.

Malam Wang Naxue ya ci gaba da cewa, bayan da 'yan kasuwa da yawa na gida da waje suka sami labarin kafa wannan sabon yankin tattalin arziki na jihar Guangxi, sun nuna sha'awarsu ainun. Bi da bi manyan rukunonin tattalin arziki da manyan kamfanonin kasa da kasa da yawa suka yi rangadin aiki a yankin. Musamman ma Mr Tsang Yam-kuen, gwamnan Hong Kong ya jagoranci tawagarsa zuwa mashigin teku na Bac Bo don yin rangadin aiki, kuma ya aika da masu aikin masana'antu sama da 80 zuwa tashar jiragen ruwa ta Fangcheng don yin ziyara.

A sakamakon ci gaba da ake samu wajen yalwata huldar abokantaka a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN cikin sauri, bangarori daban daban suna kara mai da hankali ga yankin mashigin teku na Bac Bo wanda ke hada Sin da kungiyar nan gu daya.

1  2