Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-21 18:38:31    
Gwamnatin Amurka tana shirin kara yawan sojoji a Iraki

cri

A waje daya kuma, shawarar kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki cikin dan lokaci ba ta samu kiyaya ba a kasar Amurka. Har ma a cikin wani rahoton da rukunin nazarin batun Iraki a majalisar dokokin kasar Amurka wanda ya kai suka sosai ga manufofin da gwamnatin Bush ta dauka, wannan rukuni ya nuna cewa, idan kwamandojin sojojin Amurka da ke kasar Iraki suna ganin cewa ana bukatar kara yawan sojojin Amurka domin tabbatar da halin da ake ciki a kasar Iraki, matakin kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki cikin sauri zai yi amfani.

Ya zuwa yanzu, hukumar soja ta kasar Amurka ta amince da shawarar kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki. Bisa labarin da aka bayar, an ce, Robert Gates, wanda ya hau kan mukumin ministan tsaron kasar Amurka kwanan baya ya kai wa kasar Iraki ziyara ba zato ba tsammani a ran 20 ga wata. Ya yi tattaunawa kan yiyuwar kara yawan sojojin kasar Amurka a kasar Iraki da hafsoshin rundunar kasar Amurka da ke Iraki da wane irin nauyi ne ya kamata a dora wa sojojin da za a tura su zuwa kasar Iraki. Wadannan hafsoshin Amurka ba su bayyana kiyaya ba kan shirin kara yawan sojojin Amurka a Iraki. Abin da kawai suke jin damuwa shi ne idan an kara yawan sojojin Amurka a Iraki, yawan sojojin Amurka da 'yan makamai na Iraki za su kai musu farmaki zai samu karuwa.

Amma, ko 'yan siyasa ko hafsoshin rundunar soja ta kasar Amurka ko mutanen da ke nuna goyon baya ga shirin kara yawan sojojin Amurka a Iraki dukkansu suna ganin cewa, kara yawan sojojin Amurka a Iraki shi ne kadai mataki daya daga cikin matakan daidaita batun Iraki gaba daya. Ya kamata tsare-tsaren da kasar Amurka ta dauka kan kasar Iraki su kara kulawa da batutuwan siyasa da tattalin arziki da diplomasiyya na Iraki. Sun nuna cewa, bayan sassauta halin da ake ciki a kasar Iraki, ya kamata gwamnatin Iraki ta kara bayar da gudummawarta, sojojin Iraki ma su kara samun damar shiga ayyukan soja da za a yi. A waje daya kuma, ya kamata kasar Amurka ta kara mai da hankali kan shirin raya kasar Iraki da kara samar wa mutanen Iraki guraban aikin yi.

A gun taron manema labaru da aka yi a ran 20 ga wata, shugaba Bush na kasar Amurka ya bayyana cewa, a kan batun Iraki, gwamnatinsa za ta yi hadin guiwa da jam'iyyar Republicans da jam'iyyar Dimokuradiyya, kuma za ta saurari ra'ayoyin bangarori daban-daban. Hakazalika, za ta daidaita manufarta kan Iraki cikin lokaci bisa halin da ake ciki a Iraki. (Sanusi Chen)


1  2