Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-21 18:38:31    
Gwamnatin Amurka tana shirin kara yawan sojoji a Iraki

cri

A gun wani taron manema labaru da aka yi a ran 20 ga wata, Mr. George W. Bush, shugaban kasar Amurka ya jaddada cewa, a hakika dai kasar Amurka tana bukatar karuwar yawan sojojin kasa da na ruwa har a kullum. Ya ce, ya riga ya bai wa Robert Gates, sabon ministan tsaron kasar Amurka umurnin gabatar masa da shawara kan yadda za a iya kara yawan sojojin kasar Amurka tun da wuri. A waje daya kuma, Mr. Gates wanda ke yin ziyara a kasar Iraki ya yi tattaunawa da hafsoshin kasar Amurka kan yiyuwar kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki. Sabo da haka, ra'ayoyin bainal jama'a sun nuna cewa, domin yanzu kasar Amurka tana cikin mawuyacin hali a kasar Iraki, sabuwar manufar da kasar Amurka za ta dauka kan kasar Iraki tana fitowa.

Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun nuna cewa, burin farko da wannan sabuwar manufar da kasar Amurka za ta dauka a kasar Iraki za ta cimma, shi ne yin watsi da matsalar rashin kwanciyar hankali a kasar Iraki, sa'an nan kuma, za ta mai da hankalinta kan harkokin siyasa na kasar Iraki a kai a kai domin taimakawa gwamnatin kasar Iraki kan yadda za ta cimma burin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da neman cigaba da kanta. Manazarta sun nuna cewa, akwai dalilai guda 2 da suka sa gwamnatin Bush da ta sanya aikin kara yawan sojoji a gaba kan dukkan ayyukan da za ta yi a kasar Iraki.

Da farko dai, yanzu, sojojin Amurka da ke kasar Iraki suna gamuwa da wahalhalun tabbatar da kwanciyar hankali. Yawan matsalolin tashe-tashen hankula da suke faruwa a kasar Iranki yana ta karuwa cikin sauri. A cikin irin wannan halin da ake ciki, 'yan siyasa masu dimbin yawa na kasar Amurka sun nemi gwamnatin kasar da ta kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki. Suna ganin cewa, nauyin farko da ke wuyan sojoyin Amurka da ke kasar Iraki shi ne tabbatar da zaman lafiyar jama'ar kasar Iraki da karuwar yawan sojojin Amurka a yankunan da 'yan shia da 'yan Sunni suke zama tare domin hana tashe-tashen hankulan da suke faruwa a tsakaninsu.

1  2