Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-18 17:58:00    
Kasar Sin ta dukufa kan yin mu'amala tsakaninta da kasashen waje a fannin ilmin likitancin gargajiya

cri

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya tana ganin cewa, ilmin likitancin gargajiya kaddara ce ta wayewar kan dan Adam, kuma yana daya daga cikin muhimman albarkatun kiwon lafiya. Sabo da haka, kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta sa kaimi sosai ga bunkasuwar ilmin likitancin gargajiya. Madam Malebona Matsoso, shugabar sashen hadin kai a fannin magungunan yau da kullum da kuma fasahar ilmin likitancin gargajiya na kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana cewa, "a cikin tsarin bunkasa ilmin likitancin gargajiya na duniya bisa manyan tsare-tsare da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta gabatar a shekara ta 2003, an bukaci kasashe membobin kungiyar da su tsara manufofi wajen raya likitancin gargajiya, kuma ana fatan kasashe daban daban za su iya shigad da likitancin gargajiya cikin tsarin jiyya na kasashen."

Kasar Sin ta kafa dokoki da ka'idoji kan likitancin gargajiya, kuma tana daya daga cikin kasashe kalilan da suka shigad da ilmin likitancin gargajiya cikin tsarin jiyya na kasar. Sabo da haka abubuwan da kasar Sin ta yi a wannan fanni sun samu amincewa sosai daga kungiyar kiwon lafiya ta duniya, kuma sun zama abubuwan koyi ga sauran kasashe.

Kungiyoyin bincike na kasashe masu yawa sun zo kasar Sin domin koyon yadda kasar Sin ta yi wajen kafa dokokin likitancin gargajiya da gudanar da shi da kuma shigad da likitancin gargajiya cikin tsarin jiyya na kasar. Haka kuma kasar Sin ta daddale yarjejeniya tare da kungiyar kiwon lafiya ta duniya, inda ta yi alkawarin ba da taimako ga kungiyar wajen sa kaimi ga bunkasuwar likitancin gargajiya na duniya ta hanyoyin sadarwa da fasahohi. Li Daning, mataimakin shugaban hukumar gudanar da likitancin gargajiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "kasar Sin wata memba ce ta kungiyar kiwon lafiya ta duniya, shi ya sa ya kamata ta sauke nauyin da aka dora mata a karkashin jagorancin kungiyar kiwon lafiya ta duniya wajen bunkasa harkar likitancin gargajiya, da more sakamako mai kyau da ta samu a wannan fanni tare da kasashe daban daban, da gaya wa kasashe daban daban matakan da ta dauka wajen shigad da likitancin gargajiya cikin tsarin jiyya na kasar bisa halin da kasar Sin ke ciki, ta yadda za ta iya bayar da gudummowarta." Kande Gao)


1  2