Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-18 17:58:00    
Kasar Sin ta dukufa kan yin mu'amala tsakaninta da kasashen waje a fannin ilmin likitancin gargajiya

cri

Kasashe masu yawa na duniya suna da ilmin likitancin gargajiya nasu, kamar likitancin gargajiya na kasar Sin da Yoga na kasar Indiya da dai sauransu. Ilmin likitancin gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen magance cuttuttuka da warkar da mutanen da suka kamu da cuttuttuka da kuma bunkasuwar ilmin likitanci. Amma sabo da dalilai iri daban daban, wasu daga cikinsu sun bace har ma sun gushe daga duniya. Tare da bunkasuwar kimiyya da fasaha cikin sauri da kuma kara fahimtar cuttuttuka da ra'ayoyin kiwon lafiya da hanyoyin jiyya, 'yan Adam sun gano cewa, ilmin likitancin gargajiya yana da halin musamman, har ma yana iya warware matsalolin da ba a iya warwarewa ta ilmin likitanci na zamani ba. Sabo da haka kasashe daban daban sun kara yin nazari da kuma yin amfani da ilmin likitancin gargajiya. To, a cikin shirinmu, za mu yi muku bayani kan mu'amala da kasar Sin take yi tare da kasashen waje a fannin ilmin likitancin gargajiya.

Bisa matsayinsa na ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin, har kullun ana dora muhimmanci a kansa a duk fadin kasar, sabo da haka ya samu bunkasuwa sosai. Ban da wannan kuma a karkashin kokarin da kasar Sin ta yi, yanzu likitancin gargajiya na Sin ya riga ya zama wani muhimmin kashi da ke cikin ilmin likitancin gargajiya na duniya. Shen Zhixiang, shugaban sashen hadin kai tare da kasashen waje na hukumar kula da likitancin gargajiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "kasashe masu yawa suna da ilmin likitancin gargajiya nasu, a fannonin hasashen ilmin likitancin gargajiya da kuma gwajin ilmin, likitancin gargajiya na Sin ya samu bunkasuwa sosai, shi ya sa ya samu yaduwa sosai a kasashen waje."

Tun shekaru 70 na karnin da ya gabata, a karkashin goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ta yi, likitancin gargajiya na Sin ya samu yaduwa cikin sauri a duk duniya. Bisa kidayar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu likitancin gargajiya na Sin ya riga ya samu yaduwa a kasashe fiye da 130, ana iya samun hukumomin jiyya na likitancin gargajiya na Sin fiye da dubu 50 a kasashen waje, kuma yawan masu aikin likitancin gargajiya na Sin ya zarce dubu 120. Ban da wannan kuma kasar Sin ta yi cudanya sosai tare da kasashen waje a fannonin horar da kwararrun likitancin gargajiya na Sin da yin nazari kan likitancin gargajiya na Sin da dai sauransu. A shekaru masu yawa da suka gabata, har kullum yawan dalibai da suke zuwa kasar Sin don shiga kwas din horaswa wajen likitancin gargajiya na Sin ya zama na farko a cikin dukkan dalibai da suka zo Sin domin koyon kimiyyar halitta.

1  2