A wannan rana da dare Kamfanin rediyo da talabijin da kuma kamfanin dillancin labaru na kasar suna ganin cewa , jawabin Mr. Olmert ya habaice da cewa , kasar Isra'ila tana kasance da makaman nukiliya , wannan ya sauya tsarin musamman na kasar Isra'ila a cikin shekaru 50 da suka shige . A cikin dogon lokaci ko da yaushe kasar Isra'ila ba ta amince da kuma ba ta musunta kasancewar makaman nukiliya ba .
Kofi Annan , Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da sanarwa cewa , ya yi mamaki kwarai da gaske ga jawabin da Mr. Olmert , firayin ministan kasar Isra'ila ya yi .
Masu binciken lamarin duniya sun bayyana cewa , kamar yadda Mr. Annan , babban sakataren MDD ya ce , idan kasar Isra'ila ba ta da makaman nukiliya , to , ina dalilin da ya sa babban jami'in kasar ya ce haka a fili ?
Bisa labarin da aka bayar , an ce , majalisar ministocin Mr. Olmert za ta yi taro don tattauna matsalar yadda za a warware rikicin siyasa ..
Masu binciken al'amarin duniya suna ganin cewa, bisa halin da ake ciki yanzu , an ce , ko shakka babu Mr. Olmert zai sami la'anci daga galibin kasashen duniya da kungiyoyin duniya da sassan Majalisar Dinkin Duniya da mutanen Isra'ila . Yanzu ba a san wane irin sakamakon da za a kawo wa Mr. Olmert shi kansa da kuma Kasar Isra'ila ba , sai mu ji ma gani.(Ado) 1 2
|