Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-13 16:42:03    
Jawabin da firayin ministan Kasar Isra'ila ya yi ya jawo hankalin mutanen duniya

cri

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 11 ga watan nan , Ehud Olmert , firayin ministan Kasar Isra'ila ya gana da manema labaru , inda ya sa kasarsa cikin jerin kasashe masu kasance da nukiliya. Wannan ne karo na farko da wani firayin ministan Isra'ila ya bayyana cewa , kasar Isra'ila tana da makaman nukiliya . Bayan da aka watsa wannan labarin sai ya jawo hankalin mutane a duk kasar Isra'ila . Kamfanonin watsa labaru daban daban sun bayar da labaru masu yawa kan jawabin da Mr. Olmert ya yi . Wasu shugabannin jam'iyyun dake adawa da gwamnati sun nemi Mr. Olmert da ya yi murabus daga mukaminsa . Mr. Olmert ya sake shiga cikin rikicin siyasa .

Bisa labarin da aka bayar , an ce , Gidan rediyon talabijin na kasar Jamus ya baysr da wani bidiyon da aka dauka kan ziyarar Olmert . Lokacin da ake tambaye shi kan matsalar nukiliyar Iran , Mr. Olmert ya yi amfani da Turanci ya ce , ko da yaushe kasar Isra'ila ba ta kawo barazanar kashe watakasa ba . Amma kasar Iran a bayyane ta ce , za ta kau da kasar Isra'ila Daga taswirar Duniya . Lokacin da kasar Iran take neman kasance da makaman nukiliya , shin za ka iya cewa wannan ya yi zaman daidai wa daida da kasar Faransa da Amurka da Rasha da kuma Isra'ila ?

Bayan da aka duba bidiyon , mataimakan Olmert sun mika hannaye gare shi . Ofishin firayin ministan kasar Isra'ila ya bayar da sanarwa cewa , jawabin da Mr. Olmert ya yi ba cikakke ba ne . Kamfanonin watsa labaru sun karya jawabinsa . A ran 12 ga watan nan a gun taron manema labaru da Mr. Olmert da Angela Merkel , firayin ministar kasar Jamus suka shirya , sau uku ne ya jaddada cewa , Isra'ila ba za ta shigo da makaman nukiliya da farko ba a Yankin Gabas ta tsakiya . Ya kuma karfafa magana cewa , jawabin da ya yi a gun taron manema labaru bai kauce wa manufar kasar Isra'ila kan matsalar makaman nukiliya ba .


1  2