Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-08 14:37:32    
Rashin tabbas kan mafitar aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Somali

cri

Manazarta sun bayyana cewa, a hakika za a gamu da wahalhalu da yawa wajen gudanar da wannan kudurin da kwamitin sulhu ya tsayar kan matsalar Somali.

Da farko, za a gamu da tarin wahalhalu domin kafa wannan rundunar kiyaye zaman lafiya. Ko da yake kudurin ya ba wa kungiyar AU da kungiyar IGAD ikon kafa wannan rundunar kiyaye zaman lafiya, amma yanzu kungiyar AU ta riga ta sha wahala sosai wajen aikin kiyaye zaman lafiya da take yi a shiyyar Darful ta kasar Sudan, da kyar za ta kara ba da taimako domin daidaita matsalar Somali, shi ya sa aikin kiyaye zaman lafiya na Somali musamman zai dogara bisa kungiyar IGAD.

Na 2, Kudurin da kwamitin sulhu ya tsayar bai ambata ko wane ne zai kula da wannan aikin kiyaye zaman lafiya ba, amma wannan muhimmancin abu ne sosai ga gudanar da kudurin.

Na 3, Kasashen yamma ba su mai da hankali sosai ga aikin kiyaye zaman lafiya na Somali, dukkansu ba su son aikawa da sojojinsu zuwa Somali. Amma sun fi son nade hannunsu suna kallon fadi-tashin da sauran mutane ke yi don yi dagiya da "musulmi masu ra'ayin ga-ni-kashe-ni wadanda suke cudanya da kungiyoyin 'yan ta'adda" da ke shiyyar da ake kira "kuryar Afirka".

'Yan kallo sun bayyana cewa, ko da yake ya kasance da hakikanan wahalwalu da yawa a fannin aikawa da sojojin kiyaye zaman lafiya, amma ko ta yaya, kudurin nan da kwamitin sulhu ya tsayar yana da ma'ana mai yakini, wato ya bayyana goyon bayan da kasashen duniya ke nuna wa gwamnatin wucin gadi ta Somali. Sa'an nan kuma ya bayyana cewa, kasashen duniya ba su yarda da wasu kasashen waje da su ta da wani mugun yaki ta hanyar yin neman wasu mutane wakilansu cikin kasar Somali, ta yadda za a mai da shiyyar kuryar Afirka ta zama fagen yaki nasu.  (Umaru)


1  2