Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-08 14:37:32    
Rashin tabbas kan mafitar aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Somali

cri

Kudurin da kwamitin sulhu na M.D.D. ya tsayar kwanan baya na ba wa kungiyar AU wato kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar IGAD wato kungiyar mu'amala tsakanin gwamnatocin kasashen gabashin Afirka ikon aika da rundunar sojan kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somali ya jawo martani sosai daga wajen sassa daban-daban da abin ya shafa, wannan ya kawo rashin tabbas kan makomar aikin kiyaye zaman lafiya da ake yi a kasar Somali.

Bisa kudurin kwamitin sulhu an ce, cikin ayyukan da wannan rundunar kiyaye zaman lafiya za ta yi har da duba yadda ake gudanar da yarjejeniyar da aka daddale tsakanin gwamnatin wucin gadi ta Somali da dakarun rukunonin addinai, da ba da kariya ga ma'aikatan gwamnatin wucin gadi, da bayar da horo ga sojojin gwamnatin kasar.

A ran 7 ga wata, Mr. Ali Mohamed Gedi, firayim ministan gwamnatin wucin gadi na kasar Somali ya nuna maraba ga wannan kuduri da kwamitin sulhu ya tsayar, kuma ya yi kira ga kungiyar AU da kungiyar IGAD da su share fage sosai domin aikawa da wannan rundunar kiyaye zaman lafiya tun da wuri. Ya kuma yi kashedi cewa, kasashen duniya da gwamnatin wucin gadi za su dauki matakai masu tsanani kan duk mutane masu zaman kansu ko kungiyoyi wadanda suke yin adawa ko hana aikin girke sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Somali.

Amma dakarun rukunonin addinai na Somali sun yi allah wadai da wannan kudurin da M.D.D. ta tsayar, sun ce kudurin zai kara tsananta halin da ake ciki a kasar Somali kuma zai kara kawo hasarar rayyuka da raunata jama'a.

1  2