Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 17:40:04    
Masu aikin fasaha na kasar Sin sun sami karbuwa bisa sakamakon nuna wasannin fasahohinsu a kauyuka

cri

Mataimakin shugaba din din din na hadadiyyar kungiyar adabi da fasahohi ta birnin Beijing Zhu Mingde ya taba aiki a kauyuka har cikin shekaru 8 da suka wuce, ya bayyana cewa, ta hanyar shiga cikin jama'a, masu aikin fasaha su iya ganin sabbin fuskokin manoman da suke zama a karkashin sabon halin da ake ciki, sa'anan kuma sun maido da su tamkar yadda abun misali da ake yi a dakalin nuna wasanni, ta hakan, a sa mutanen da ke kara yawa suke yi su sami himma da wayewar kai da gamsuwa da dai sauransu.

Zaman rayuwar manoma sai kara kyautatuwa yake yi a kasar Sin, shi ya sa manoma suna kara nuna sha'awarsu a kan shagulgulan al'adu, kodayake a kauyuka da akwai wadanda suke kishin wasannin fasaha da yawa, kuma suna kan shirya nune-nunen zane da shagulgulan wake-wake da raye-waye da dai sauransu, amma suna son samun horo daga wajen kwararru. Saboda haka a wannan gamin da aka nuna wasanni a kauyen Bai Yu, wasu kwararru sun ba da horo ga wasu manoma wajen nuna wasannin kwaikwayo.

Manoma sun bayyana cewa, masu aikin adabi da fasaha sun shiga cikinmu, kuma sun bayyana wasanninsu gare mu, wannan ya yi daidai da nuna mana kulawa sosai, yada fasahohinsu ke kara wayar da kanmu sosai, ya sa kaimi ga raya wasannin kwaikwayo na kauyenmu, kuma wannan ne babban taimako gare mu.

Wani manomi mai suna Chen Yonglu ya bayyana cewa, ya yi fatan za su kara samun jagoranci daga wajen kwararru a lokacin da suke nuna wasannin fasaha ta yadda za a iya yada wasannin kwaikwayon da suke kauna sosai duk domin wadatar da zaman rayuwar manoma.(Halima)


1  2