Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 17:40:04    
Masu aikin fasaha na kasar Sin sun sami karbuwa bisa sakamakon nuna wasannin fasahohinsu a kauyuka

cri

Kwanan baya, an yi babban taro na 8 na wakilan hadadiyyar kungiyar rukunonin adabi da fasahohi ta kasar Sin da babban taro na 7 na wakilan hadadiyyar kungiyar mawallafa na kasar Sin a birnin Beijing. A gun tarurukan biyu da aka yi, an bayyana sakamakon da kasar Sin ta samu wajen sha'anin adabi da fasahohi a cikin shekaru biyar da suka wuce, kuma an gabatar da shawara ga dimbin masu aikin adabi da fasahohi na kasar Sin da su shiga cikin jama'a don neman labaransu da kuma gabatar da wasannin fasahohi gare su. Kafin taron, masu aikin adabi da fasaha na birnin Beijing sun taba nuna wasannin fasahohinsu a gundumomi da garurukan da ke kewayen birnin Beijing, saboda haka sun sami karbuwa sosai daga wajen jama'ar wuraren .

Jama'a masu sauraro, abin da kuke saurara yanzu shi ne wasan 'yan kama da aka yi, a cikin wata babbar rumfa mai sauki da ke a wani kauye mai suna Bai Yu na birnin Beijing, 'yan wasannin fasaha na birnin Beijing suna nan suna nuna wasannin fasaha, 'yan kallo na kauyen da yawan gaske sun cika rumfar suna kallon wasannin, sun yi farin ciki sosai, har ma suna ta barka da dariya a wasu lokatai.

Mr Li Zengrui mai shekaru 59 da haihuwa, ya soma nuna wasannin 'yan kama a shekarar 1960, a yawancin lokatansa, ya kan nuna wasanninsa ga ma'aikatan ma'adinai, a kauyen Bai Yu, lokacin da ya ga jama'ar wurin sun nuna kauna sosai ga wasanninsu, sai ya yi farin ciki sosai, ya bayyana cewa, mutane suna son kallon wasannin 'yan kama, wannan ya bayyana cewa, karfin rayuwar wasannin 'yan kama ya bayyanu ne a cikin jama'a , idan mutane suna son irin wannan wasa, to ana iya fada cewa, wasan nan na da karfin rayuwa. Ya kamata mu shiga cikin jama'a don kara karfin rayuwar wasanninmu.

1  2