Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 09:11:55    
Kasar Quatar tana fatan kungiyar wakilan kasar Sin za ta samu cikakkiyar nasara a gun taron wasannin Asiya

cri

Kasar Quatar wata karamar kasa ce dake shiyyar tekun parisa,tana da yawan mutane fiye da dubu dari 7 kawai,A cikin `yan shekarun da suka shige,bisa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al`umma,sha`anin wasannin motsa jiki na kasar shi ma ya samun bunkasuwa cikin sauri,A gun taron wasannin Asiya na Busan,kungiyar wakilan kasar Quatar ta samun lambobin zinariya 4 da na azurfa 5.A halin da ake ciki yanzu,sha`anin wasannin motsa jiki na jama`a wato ba na sana`a ba shi ma ya samun yalwatuwa a bayyane.A duk fadin kasar,gaba daya akwai kungiyoyin wasannin motsa jiki na matsayin kasa 26 da club din na wasannin motsa jiki 16.A gun taron wasannin Asiya da ake yi yanzu,ana yin amfani da hadadden filayen wasanni da dakunan wasanni fiye da 20,daga baya kuma wato bayan wannan taron wasannin Asiya,za a bude yawancin wadannan wurare ga mazauna birnin.

Kan wannan,Mr.Saoud ya yi nuni da cewa,kasar Quatar ba ta da mutane da yawa,shi ya sa akwai wuya wajen zaben `yan wasa,ya ce:  `Idan kasar Sin ta zabi `yan wasa 200,za ta iya zabi saura da yawa,amma a kasar Qutar,ba haka ba ne,shi ya sa dole ne a darajanta karfin `yan wasa.`

Mr.Saoud ya yi mana bayani cewa,a gun wannan taron wasannin Asiya,kasar Quatar za ta samu babban sakamako.Ban da wannan kuma,Mr.Saoud shi ma ya nuna gamsuwarsa ga huldar hadin gwiwa wajen wasannin motsa jiki tsakanin kasar Sin da Kasar Quatar.Ya ce,ya kasance da hulda mai kyau tsakanin kasashen nan biyu,muna farin ciki kwarai da gaske saboda za a shirya zama na 16 na taron wasannin Asiya a birnin Guangzhou na kasar Sin,bari mu yi kokari tare.(Jamila Zhou)


1  2