Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 09:11:55    
Kasar Quatar tana fatan kungiyar wakilan kasar Sin za ta samu cikakkiyar nasara a gun taron wasannin Asiya

cri

Ran 1 ga wata,an bude zama na 15 na taron wasannin Asiya a birnin Doha na kasar Quatar,gaba daya `yan wasa fiye da dubu goma da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 45 sun shiga manyan gasanni 39 da aka shirya,yawan lambobin zinariya na gasannin ya zarce 400.Kafin budewar wannan taron wasannin Asiya,wakilinmu ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar din-din-din na kwamitin wasannin Olimpic na kasashen Asiya kuma babban sakataren kwamitin wasannin Olimpic na kasar Quatar Sheikh Saoud Bin Abdulrahman Al-Thani domin jin ta bakinsa,Mr.Saoud ya gaya wa wakilinmu cewa,ko shakka babu kungiyar wakilan kasar Sin da ta kasa mai masaukin baki wato kasar Qutar za su samun cikakkiyar nasara a gun taron wasannin Asiya da ake yi.Yanzu bari mu yi muku bayani kan wannan.

A gun taron wasannin Asiya da aka shirya a da,kungiyar wakilan kasar Sin ta taba samun lambobin zinariya mafiya yawa sau shida,musamman a gun taron wasannin Asiya da aka yi a birnin Busan a shekarar 2002,gaba daya kungiyar wakilan kasar Sin ta samun lambobin zinariya da yawansu ya kai 150.Mr.Saoud ya bayyana cewa,kasar Sin ita ce babbar kasa ta wasannin motsa jiki,`yan wasan kasar Sin suna da fasahohin manyan gasanni da yawa kuma kasar Sin tana da fitattun `yan wasa da yawa.A kullum `yan wasa na kasar Sin sun samun lambobin zinariya da yawan gaske.A gun taron wasannin Asiya na Doha,tabban ne za su ci gaba da samun lambobin ziyariya da yawa.A sa`i daya kuma,kasar Sin tana yin amfani da wannan taron wasannin Asiya domin horar da `yan wasanta,wato tana yin aikin share fage musamman domin taron Olimpic na Beijing na shekarar 2008.Game da wannan,Mr.Saoud ya ce: `A ganina,kasar Sin ta tura kwararrun `yan wasa zuwa birnin Doha domin shiga gasanni,dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin tana so ta duba halin da suke ciki daga dukkan fannoni.`

Mr.Saoud ya ce,`yan wasa na kasar Sin su ne fitattun `yan wasa,ya ci gaba da cewa,a shekarar 2004,yawan lambobin zinariya da kasar Sin ta samu ya zama lambatu a gun taron wasannin Olimpic na Athen,ya ce:  `A Athen,`yan wasa na kasar Sin sun yi takara da `yan wasa na kasar Amerka,`yan wasa na kasar Sin sun yi kokari amma a karshe dai,saboda karfinsu wajen gasannin guje-guje da tsalle-tsalle bai kai na `yan wasa na kasar Amerka ba,shi ya sa yawan lambobin zinariya da suka samu sun zama lambatu kawai.amma yanzu,na dauka cewa,kasar Sin za ta zama zakara a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008.Haka ne.`

1  2