Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 09:09:59    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (29/11-06/12)

cri

Ran 29 ga watan jiya,hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasashen Asiya ta yi bikin ba da lambobin yabo ga `yan wasa da suka fi nagarta na shekarar 2006 a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular Larabawa,`yar wasa daga kasar Sin Ma Xiaoxu ta samu lambar yabo ta `mace ta kwallon kafa ta Asiya`,a sa`i daya kuma,Ma Xiaoxu ita ma ta samu lambar yabo ta sabuwar `yar wasa mafi nagarta ta kasashen Asiya ta shekarar 2006.

Daga ran 30 ga watan jiya zuwa ran 3 ga wata,an yi gasar ba da babbar kyauta ta wasan kankara salo-salo ta hadaddiyar kungiyar wasan kankara ta duniya tsakanin shekarar 2006 da shekarar 2007 a birnin Nagano na kasar Japan,`yan wasa daga kasar Sin Shen Xue da Zhao Hongbo da kuma Zhang Dan da Zhang Hao sun samu lambobin zinariya biyu na wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji.(Jamila Zhou)


1  2