Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 09:09:59    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (29/11-06/12)

cri

Ran 1 ga wata,an bude zama na 15 na taron wasannin Asiya a birnin Doha,babban birnin kasar Quatar,wannan shi ne karo na biyu da aka shirya taron wasannin Asiya a shiyyar dake yammacin Asiya,shi ma karo na farko ne da aka shirya taron a kasar Larabawa.Gaba daya `yan wasa fiye da dubu goma da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 45 sun shiga gasanni domin neman samun lambobin zinariya da yawansu ya kai 424.Kasar Sin ta tura wata kungiyar wakilai wadda ke kumshe da mutane fiye da 900.Za a kammala taron a ran 15 ga wata.

Ran 3 ga wata,a cikin gasar wasan daukan nauyi na ajin kilo 58 na mata da aka yi a gun taron wasannin Asiya na Doha,`yar wasa daga kasar Sin Chen Yanqing ta kago wani sabon matsayin bajimta na duniya da kilo 251.

Ran 29 ga watan jiya,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya sanar da farashin tikitin kallon gasannin Olimpic na shekarar 2008,farashin yawancinsu bai kai kudin Sin Yuan 100 ba,wato ya fi na da araha.Kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya bayyana cewa,dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin ita ce kasa mai tasowa,kudin shiga na jama`ar kasar ba shi da yawa.

1  2