Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-04 17:09:10    
Kwas din horaswa na farko da kasar Sin ta shirya wajen hana cutar murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane

cri

Bisa matsayinta na wata sabuwar cutar da ta fi saukin harbar mutane, murar tsuntsye ta riga ta zama wani abin da ke jawo hankulan mutane sosai a duk duniya. a watan Oktoba na shekara ta 2005, yaron farko da aka tabbatar da ya kamu da murar tsuntsaye a kasar Sin an kai shi asibitin yara na jihar Hunan, kuma sakamakon matakan da aka dauka a jere, yaron ya samu warkewa sosai bayan kwanaki fiye da 10. Ban da wannan kuma a watan Fabrairu na shekara ta 2006, asibitin ya warkar da wani yaro mai shekaru 6 da haihuwa wanda ya kamu da cutar. Sabo da haka aisibitin ya jawo hankulan mutane na duk duniya sosai, kuma hukumar kiwon lafiya ta duniya da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin sun amince da sakamakon da ya samu sosai a wannan fanni, haka kuma sakamakon ya zama muhimmin abu ne da ke cikin wannan kwas din horaswa.

Madam Zhu Lihui, mai kula da harkokin kwas din horaswa ta bayyana cewa, "mu ba da darusa ta hanyoyi uku, na farko shi ne malamai sun yi lacca kan rigakafin murar tsuntsaye da warkar da cutar, da kuma yadda ya kamata a warware matsala idan sun gamu da mutanen da suka kamu da cutar. Na biyu shi ne gwajin aiki, wato sun je asibiti da kansu don lura da halin da mutanen da suka kamu da cutar ke ciki. Ban da wannan kuma za mu ba su wasu lotuka domin su yi mu'amala tsakaninsu."

A cikin wannan kwas din horaswa, ana dora muhimmanci kan sabbin fasahohi iri daban daban wajen warkar da mutanen da ke kamuwa da murar tsuntsaye. Ta horon da aka yi, mutanen da suka shiga kwas din horaswa za su samun ilmi da yawa dangane da murar tsuntsaye da ta yadu tsakanin mutane, kuma za su iya koyi da sakamako mai kyau da asibitin yara na jihar Hunan ya samu wajen yi wa mutanen da suka kamu da murar tsuntsaye jiyya cikin gagawa.

A 'yan kwanakin da suka gabata, mutanen da aka horar da su sun nuna yabo sosai ga kwas din horaswar. Madam Phone Davann da ta zo daga kasar Laos ta bayyana cewa, "na ji farin ciki sosai da na iya shiga kwas din horaswa. Ko da yake lokacin kwas din horaswa gajere ne, amma muna iya koyi da sakamako mai kyau da juna, wannan zai ba da taimako sosai ga ayyukanmu wajen hana murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane." Kande Gao)


1  2