Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-04 17:09:10    
Kwas din horaswa na farko da kasar Sin ta shirya wajen hana cutar murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane

cri

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kwararrun shawo kan cuttuttuka da jami'ai masu kula da kiwon lafiya na kasashe masu tasowa 17 na nahiyoyin Asiya da Amurka da kuma na Afirka sun zo asibitin kula da yara na jihar Hunan da ke kasar Sin domin shiga wani kwas din horaswa na kasa da kasa da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya domin hana cutar murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane. Wannan yana daya daga cikin muhimman ayyukan da kasar Sin ta shirya domin ba da taimako ga kasashe masu tasowa, kuma shi ne kwas din horaswa na kasa da kasa na farko da kasar Sin ta shirya wajen hana cutar murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane, wanda zai taka muhimmiyar rawa ga ayyukan hana murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane a duk duniya. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan kwas din horaswa.

Za a yi wannan kwas din horaswa na kasa da kasa har kwanaki 40, kuma za a waiwaya domin duba sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu wajen hana murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane, musamman ma habaka sakamako mai kyau da kuma dabarun zamani da asibitin yara na jihar Hunan a wannan fanni, ta yadda za su iya taimaka wa kasashe masu tasowa wajen daga matsayin fasahar hana murar tsuntsaye yaduwa tsakanin mutane, da kuma sa kaimi ga kwarewar masu shiga kwas din horaswa wajen aiki don rage yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar. Shugaban asibitin yara na jihar Hunan Zhu Yimin ya bayyana cewa, "muna gano cewa, mutane na kasashe masu tasowa da kuma na kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya sun fi samun saukin kamuwa da cutar murar tsuntsaye, sabo da haka mun shirya wannan kwas din horaswa don kasashe masu tasowa, a waje daya kuma wannan wani muhimmin aiki ne wajen hadin gwiwa tsakanin mutane masu fasaha kan cutar murar tsuntsaye na kasar Sin da kasashe masu tasowa. Bisa halin yaduwar murar tsuntsaye tsakanin mutane da ake ciki, muna gano cewa, mutane sun fi samun saukin kamuwa da cutar a lokacin hunturu da kuma lokacin bazara, sabo da haka ne muka zabi wannan lokaci wajen shirya wannan kwas din horaswa."

1  2