Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-24 18:58:45    
Masana sun tattauna dangantakar da ke tsakanin bunkasa hakkin dan Adam da raya duniya mai jituwa

cri

A gun taron, Li Yunlong na kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ya gabatar da cewa, raya duniya mai jituwa yana bukatar kasashen duniya da su tattauna da yin hadin gwiwa kan hakkin dan Adam daga fannoni daban daban, sa'an nan kuma, yin tattaunawar hakkin dan Adam yana da amfani wajen tabbatar da raya duniya mai jituwa.

Wannan ra'ayi ya sami amincewa daga wasu kwararrun kasashen waje. Shehun malami Roberto Saba na kasar Argentina ya bayyana cewa,'Muna ganin cewa, wajibi ne a canja matakan da ake dauka a fannin hakkin dan Adam. Da can, mu kan yi wa wasu kasashe suka saboda ba su kula da hakkin dan Adam yadda ya kamata, yanzu ya kamata mu dora muhimmanci kan yin tattauanwa dangane da kiyaye hakkin dan Adam. Wani dalilin da ya sa ake saba hakkin dan Adam shi ne domin karancin musayar bayanai da fahimtar juna, shi ya sa yin tattaunawa babbar hanya ce mai muhimmanci wajen warware wannan batu, yana amfanawa sa kaimi kan kasashen duniya da su girmama hakkin dan Adam.'

Ban da wannan kuma, masanan kasashen waje sun bayyana ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin bunkasa hakkin dan Adam da tabbatar da raya duniya mai jituwa bi da bi. Miguel Martinez, wani masani na kasar Brazil, ya bayyana cewa, shimfida jituwa a wata kasa yana bukatar tabbatar da hakkin dan Adam daga dukan fannoni, kuma shimfida jituwa a duniya yana bukatar girmama ikon mulkin kasashen duniya cikin daidai wa daida, raya duniya mai jituwa muhimmin sharadi ne wajen tabbatar da jituwa a wata kasa.

A gun bikin rufe taron kara wa juna ilmi da aka yi, mataimakin shugaban kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin Jin Jian ya yi jawabi a madadin dukan masu halartar taron. Ya ce, 'Wakilai masu halartar taron muna ganin cewa, raya duniya mai jituwa ya hada da muhimman abubuwa ta fuskar kimiyya, duniya mai jituwa wuri ne da ya dace da mutane da su yi zama tare, kuma ya cancanci dukan mutanen kasashen duniya da su yi kokari don samun wannan wuri. Rashin girmamawa da ba da tabbaci ga hakkin dan Adam ya kan haifar da abubuwa masara jituwa a duniya, shi ya sa ingiza ci gaban hakkin dan Adam hanya ce mai amfani wajen kawar da rashin jituwa da kuma tabbatar da raya duniya mai jituwa.'(Tasallah)


1  2