Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-24 18:58:45    
Masana sun tattauna dangantakar da ke tsakanin bunkasa hakkin dan Adam da raya duniya mai jituwa

cri

Ran 24 ga wata, a nan Beijing, an rufe taron kara wa juna ilmi kan 'girmama da bunkasa hakkin dan Adam da kuma raya duniya mai jituwa' da aka yi kwanaki 3 ana yinsa. Masana da kwararru masu kula da hakkin dan Adam fiye da 70 daga kasashe da yankuna misalin 20 sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin bunkasa hakkin dan Adam da raya duniya mai jituwa, suna ganin cewa, bunkasa ci gaban hakkin dan Adam hanya ce mai amfani wajen kawar da rashin jituwa da tabbatar da kafa duniya mai jituwa.

A gun taron shugabanni don taya murnar cikon shekaru 60 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a watan Satumba na shekarar 2005, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi mai lakabi haka 'a yi kokari wajen raya duniya mai zaman lafiya da wadatuwa da jituwa cikin dogon lokaci'. Ra'ayin raya duniya mai jituwa ya zama daya daga cikin batutuwan da ke jawo hankulan masana na gida da na waje. A gun wannan taro da aka yi, masu halartar taron sun yi tattaunawa sosai kan dangantakar da ke tsakanin bunkasa hakkin dan Adam da raya duniya mai jituwa.

Shehun malami Chang Jian na Jami'ar Nankai ta kasar Sin wanda ya wakilci masanan kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa. Ya yi bayanin cewa, tabbatar hakkin dan Adam muhimmin abu ne da aka tanada cikin aikin raya duniya mai jituwa, kuma muhimmin tushe ne na wannan aiki, sa'an nan kuma, samun duniya mai jituwa makasudi da sharadi ne wajen tabbatar da hakkin dan Adam. Yin gasar jan damara da nuna fin karfi a fannin siyasa da ra'ayin daukan matakin gashin kai da ta'addanci da sabuwar darikar Nazi da babban gibi da ke tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni da kuma gurbata muhalli dukansu cikas ne wajen raya duniya mai jituwa. Ya kamata a yi tattaunawa a maimakon nuna kiyayya, kuma a hada kai a maimakon ta da hargitsi a fannin raya duniya mai jituwa. Ya ce,'Abu mafi muhimmanci wajen raya duniya mai jituwa shi ne ka'idar girmama ikon mulkin kasa cikin daidai wa daida. Ya kamata a girmama juna a fannin siyasa, da taimaka wa juna a fannin tattalin arziki, da yin koyi da juna a fannin al'adu, da hada kan juna a fannin tsaron kai, da kuma amincewa da muhimmancin tabbatar da hakkin dan Adam ta fuskar tarihi da daukan matakai sannu a hankali.'

1  2