Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-21 17:37:44    
Gundumar Fengyang ta lardin Anhui na kasar Sin

cri

Mr. Xia ya kara da cewa, da can don koma gida, mutane su kan rike da wata karamar ganga a hannu na hagu, su buga gangar da sanduna 2 na gora sirara masu tsawo da ke hannunsu na dama, su rera wakar Fengyang tare da kide-kiden ganga, su nuna wasan kwaikwayo don neman samun kudi tare da yin bara a kan hanyarsu ta komawar gida.

Masu yawon shakatawa da suka ziyarci Fengyang su kan sayi gangunan Fengyang kamar abun tunawa, sun kuma yo sha'awar kallon gangunan kasar Sin iri daban daban da aka nuna a cikin hasumiyar hange ta Zhongdu na Fengyang, wadanda suka hada da gangar Fengyang. Xie Lan, mai yi karin haske, ta ce, 'Muna da manyan ganguna 11 a nan, ganga mafi girma da ke cikinsu diameter nata ya kai mita 2, an samar da ita da wata fatar shanu duka. Sauran 10 kuma diameter nasu ya kai mita 1.5. Mun sanar da babban zaure na kungiyar kula da matsayin bajimta ta duniya wato Guinnes sworld records da ke birnin Shanghai cewa, wannan babbar ganga ta zama ganga mafi girma a duk duniya. Haka kuma wata karamar gangar da diameter nata ya kai santimita 2 kawai ta zama ganga mafi karama a duk duniya.'

Yanzu hukumar gundumar Fengyang ta yayata al'adu da tarihi na Fengyang da albarkatun yawon shakatawa na Fengyang ta hanyar yayata wasan kwaikwayon gangar Fengyang. An tanadi wasan kwaikwayon gangar Fengyang a cikin takardar sunayen abubuwan tarihi na al'adu da ba su kai na a-zo-a-gani ba ta kasar Sin a watan Yuni na shekarar bana. Bugu da kari kuma, an yi bikin yawon shakatawa na al'adun wasan kwaikwayo na gangar Fengyang na kasar Sin a karo na farko a Fengyang a watan Satumba na wannan shekara.

Shugaban gundumar Fengyang Fan Dijun ya yi bayanin cewa, a shekarar 2002, hukumomin kasar Sin da abin ya shafa sun yi shirin yin amfani da kudin RMB misalin miliyan 86 wajen yin kwaskwarima kan wurin tarihi na birnin Zhongdu. Ana yin kwaskwarima bisa manufofin kara kiyaye wuraren gargajiya, da bayyana nufin shiryawa na da, da yin amfani da kasa da gine-ginen tarihi da kuma ruwa yadda ya kamata, da kuma yin amfani da albarkatun yawon shakatawa yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, an canja gonakin da ke cikin birnin zuwa lambuna, tare da sharadi na farko wato bisa nufin shiryawa na da da kuma karfafa ingancin muhalli, ta yadda dasa bishiyoyi a cikin birnin ya yi nasaba da ribar da aka samu daga yawon shakatawa da muhalli da kuma tattalin arziki.


1  2