Idan an tabo magana kan gundumar Fengyang na lardin Anhui, da farko dai Sinawa su kan tuna da sarkin zamanin daular Ming wato Zhu Yuanzhang, wanda aka haife shi yau da shekaru fiye da 600 da suka wuce, shi kuma ya hambarar da gwamnatin daular Yuan, ya kafa gwamnatin daular Ming. A farkon kafuwar gwamnatin daular Ming, Zhu Yuanzhang ya tattara 'yan kwadago masu fasaha miliyoyi, su yi shekaru 6 suna gina birnin Zhongdu a Fengyang.
Amma a yayin da ake kusan kammala kafa birnin Zhongdu, Zhu Yuanzhang ya yi watsi da wannan birni ba zato ba tsammani. Yanzu wurin tarihi na birnin Zhongdu da ba a gama gina shi ba yana ci gaba da kasancewa a Fengyang, masanan da abin ya shafa sun mayar da shi a matsayin misalin ginawa na fadar sarakuna ta Beijing, wato Forbidden City. Wannan kuma tahiri ne da mazaunan wurin suka ji alfahari game da shi.
Girma da alatu na birnin Zhongdu sun fi na fadar sarakuna ta Beijing a fannoni daban daban. An gaji salon gine-gine na gargajiya na kasar Sin, sa'an nan kuma an sabunta a lokacin da aka gina wannan birni, shi ya sa yana da muhimmanci sosai a cikin tarihin bunkasuwar gine-gine na biranen zamanin da na kasar Sin. Masani mai ilmin tarihin zamanin daular Ming na cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin Xia Yurun ya yi karin haske cewa, bullowar wasan kwaikwayo na gangunan Fengyang tana da nasaba da wannan birni. Ya ce, 'Don kara yawan mazaunan babban birni, Zhu Yuanzhang ya tsai da kudurin kaurar da mutane daga sauran wuraren kasarsa, wadanda suka hada da mutane na rukunnoni daban daban, 'yan kudu da 'yan arewa da 'yan kabilar Han da 'yan kananan kabilun kasar, yawansu ya kai kimanin 600,000. Aikin kaura da Zhu Yuanzhang ya yi aikin kaura ne mafi girma a cikin tarihin kasar Sin, sa'an nan kuma ya shafi mutane mafi yawa, wadanda suka zo daga rukunoni mafi yawa. Amma ba a gama gina birnin Zhongdu ba, shi ya sa bayan da Zhu Yuanzhang ya rasu, talauci ya fara bayyana a Fengyang sannu a hankali, tun daga shekarar 1437, mazaunan Fengyang da yawa suka fara yin bara, muna ganin cewa, wasan kwaikwayo na gangunan Fengyang ya fito tun daga shekarar 1436 zuwa shekarar 1450. '
1 2
|