Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 21:41:30    
Ziyarar Hu Jintao a kasashe 4 na Asiya tana da babbar ma'ana

cri

Hu Jintao , babban sakataren Jam'iyyar kuma shugaban kasar ya kai ziyarar aiki a kasar Laos . Wannan kuma karo na farko ne da aka zabi sabbin shugabannin jam'iyya da gwamnatin kasar Laos . Bayan da aka yi shekaru 6 , shugaban kasar Sin ya sake kai ziyara a kasar Laos . Muna fatan ta hanyar wannan ziyara , za a karfafa zumunci da hadin gwiwa kuima za a shirya makomar dangantaka tsakanin bangarorin biyu .

Kasar Sin da kasar India manyan kasashe masu tasowa ne . Kuma manyan kasashe na Asiya . A cikin 'yan shekarun da suka wuce , shugabannin kasashen biyu sun kai wa juna ziyara kuma sun karfafa amincewar siyasa . Hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen biyu sun sami bunkasuwa da saurin gaske . A watan Afrilu na shekarar 2005 , Wen Jiabao , firayin ministan kasar Sin ya kai ziyara a kasar India . Kasashen biyu sun sanar da cewa za su kafa huldar abokai na tsarin musamman don zaman lafiya da wadatuwar Asiya da duniya . Wannan ya bayyana cewa , dangantaka tsakanin kasashen 2 ta shiga sabon mataki . Mr. Cui ya bayyana cewa ,

Ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a kasar India karo na farko ne da shugaban kasar Sin zai yi a cikin shekaru 10 da suka shige. Muna amince da cewa , wannan ya bayyana ga kasashen duniya cewa , bunkasuwar kasar Sin da kasar India ba kawai ta samar da sabuwar dama ga hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ba , har ma za ta ba da taimako sosai ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da yalwatuwar duniya .

Tun daga shekaru 55 da kasar Sin da Pakistan suka kulla huldar diflomasiya sun riga sun yi hadin gwiwa sosai a wajen siyasa da tattalin arziki da aikin soja da kimiyya da fasaha da al'adu da sauran fannoni . Hulda tsakanin kasashen biyu ta riga ta zama misali na kasashe wadanda suke da tsarin mulki mai bambanci da kuma al'adu masu shan banban .

Shugaba Hu Jintao zai halarci taron shugabannin Kungiyar APEC . A gun taron zai gana da shugaba Bush na kasar Amurka da Abe Shinzo , firayin ministan kasar Japan da sauran shugabannin kasashen, kuma za su musanya ra'ayoyinsu kan hulda tsakanin bangarori biyu-biyu da matsalolin shiyya-shiyya da duniya wadanda suke jawo hankulansu.(Ado )


1  2