Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 10:59:49    
An tabbatar da sabon dan takarar mukamin firayin ministan Palesdinu

cri

Da zarar malam Shubair ya zama firayin ministan Palesdinu, muhimmin kalubalen da ke gabansa shi ne ba ma kawai ya kamata sabuwar gwamnati ta sami amincewa daga bangarori daban-daban ba, har ma dole ne ta biya bukatun kasashen duniya. Jama'ar Palesdinu suna fatan sabuwar gwamnati za ta iya kawar da ra'ayoyin nuna bambanci daga bangarori daban-daban, kuma za ta kawo karshen rikice-rikicen zubar da jini iri iri a kasar domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'ummomin kasar. A waje daya kuma, dole ne sabuwar gwamanti ta samu amincewa daga kasashen duniya domin sake neman taimakon kudin waje da aka dakatar da su har na tsawon fiye da rabin shekara. Sakamakon haka, za a iya sassautar matsalar rashin kudi da ake ciki yanzu a Palesdinu, sabuwar gwamnati ma za ta iya yin aiki kamar yadda ya kamata.

Yanzu, kasar Isra'ila da muhimman kasashen yammacin duniya suna maraba da kafuwar wata hadaddiyar gwamnati a Palesdinu. Amma dukkansu sun jaddada cewa, dole ne sabuwar gwamnatin Palesdinu ta biya bukatu 3 na kasashen duniya, sannan kuma ta amince da Isra'ila, kuma ta yi watsi da matakan hare-hare har ta amince da dukkan yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka kulla a da a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Lokacin da yake ganawa da wakilin wata jaridar Palesdinu, Mr. Ehud Olmert, firayin ministan Isra'ila ya ce, muddin kungiyar Hamas ta amince da wadannan sharuda 3, zai yi shawarwari da sabuwar gwamnatin Palesdinu da ke da membobin kungiyar Hamas. Kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai, muhimman bangarori biyu ne da ke samar wa Palesdinu taimakon kudi, sun kuma bayyana cewa, idan sabuwar gwamnatin Palesdinu ta amince da wadannan sharuda 3, za su ci gaba da samar wa Palesdinu taimakon kudi.

Har yanzu, hukumar Palesdinu ba ta sanar da nadin Shubair a hukunce ba, malam Shubair ma ya ce, har yanzu bai samu takardar nadi a hukunce ba. A waje daya kuma, dole ne irin wannan nadi ya fara aiki bayan samun aimincewa daga Mahmoud Abbas, shugaban hukumar ikon mulkin al'ummar Palesdinu. Tsohon firayin minista Ahmed Qurie na Palesdinu ya ce, a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, halin siyasa da ake ciki a kasar Palesdinu zai samu sauye-sauye sosai, kasar Palesdinu ma za ta shiga wani sabon lokaci. (Sanusi Chen)


1  2