Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 10:59:49    
An tabbatar da sabon dan takarar mukamin firayin ministan Palesdinu

cri
A ran 13 ga wata, kungiyar Hamas da kungiyar Fatah na kasar Palesdinu sun sami ra'ayi daya kan batun tabbatar da sabon dan takarar mukamin firayin ministan hadaddiyar gwamnatin kasar Palesdinu, inda suka yarda da Mohamed Shubair, tsohon shugaban jami'ar Islamic ta Gaza, ya zama sabon firayin ministan hadaddiyar gwamnatin Palesdinu. Wani babban jami'in kungiyar Hamas ya ce, malam Shubair ya riga ya amince da wannan nadi. Daga karshe dai bangarorin Palesdinu daban-daban sun sami ra'ayi daya kan batun kafa wata hadaddiyar gwamnatin al'ummar Palesdinu bayan da aka yi shawarwari da rikice-rikicen zubar da jini har na tsawon rabin shekara a tsakaninsu.

A shekarar 1946 ne aka haifi Mohamed Shubair a zirin Gaza. Ya kuma koyi ilmin likitanci a kasar Masar. Sa'an nan kuma ya sami digiri na 3 a jami'ar West Virginia ta kasar Amurka. Daga baya ya koma zirin Gaza ya zama shugaban kwalejin koyon ilmin likitanci na jami'ar Islamic ta Gaza. Tun daga shekarar 1993 ne ya hau kan mukamin shugaban jami'ar Islamic ta Gaza har ya yi ritaya a shekarar da ta gabata.

Ana ganin cewa, malam Shubair ba shi da ra'ayoyi masu tsanani domin bai shiga kowace jam'iyyar siyasa ba. Yana da kyakkyawar hulda da kunigyar Hamas da ta Fatah duka. Bugu da kari kuma, malam Shubair mutum ne da yake daidaita harkoki iri iri bisa halin da ake ciki, kuma bai taba yin sharhi kan matsayinsa game da Isra'ila a fili ba. Amma lokacin da yake ganawa da wakilin jaridar Haaretz ta kasar Isra'ila, ya taba bayyana cewa, tana da kyakkyawar hulda da bangarori daban-daban, ciki har da kasar Amurka. Idan an nada shi firayin ministan Palesdinu, zai dauki matakan da za su dace da halin da ake ciki.

Wani jami'in Palesdinu ya ce, idan an nada malam Shubair a hukunce, zai shugabanci wata majalisar ministoci da ke kushe da kusan dukkan mutane masu 'yancin kai. Yanzu, kungiyar Hamas da kungiyar Fatah suna shawarwari kan 'yan takarar mukaman ministoci da batun raba ikon sabuwar gwamnati. An bayar da labari cewa, kungiyar Hamas za ta gabatar da ministoci 10 tare da kungiyar Fatah ta gabatar da ministoci 5.


1  2