Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 16:18:28    
Sojojin kasar Sin suna kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia

cri

Bisa bayanin da aka yi , an ce , wadannan sojojin sun zo ne daga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin . Saboda kasar Liberia ta yi yakin basasa cikin shekaru masu yawa , shi ya sa hanyoyin suka lalace . Sojojin kasar Sin sun yi aiki mai nauyi . Su kan aiki a daji cikin jerin wasu watanni . Chen Dajun , mataimakin kyaftin na Kungiyar sojoji masu lalata nukiyoyi ya gaya wa wakilinmu cewa , a wurin nan da kyar mun gyara hanyoyi . Wani lokaci wata hanyar da muka gyaru ba da dadewa ba , da aka yi ruwa , sai ta zama tabo . Yanzu bayan da sojojin kasar Sin suka yi ta yi kokari , hanyar ta riga ta zama hanyar zirga-zirga wadda motoci ke iya gudu da saurin kilomita 60 zuwa 80 cikin awa . Christopher Bailey , shugaban Jihar Grand Gedeh ya nuna godiya kwarai da gaske ga sojojin kasar Sin . Ya ce , huldar dake tsakanin mu da sojojin kasar Sin mai jituwa ce . Muna kaunarsu kuma muna zama kamar yadda 'yan iyali ke zaman rayuwa .

Bayan haka wakilin rediyonmu ya kai ziyara a Sashen masu jiyya na sojojin kasar Sin . A cikin wannan Sashen akwai mutane 43 . Ko da ya ke mutane ba su da yawa , amma duk da haka suna daukar nauyin warkar da sojoji kusan dubu 5 na wurin da mutanen farar hula . Sun Tiansheng , shugaban Kyaftin Kungiyar jiyya ya gaya wa wakilinmu cewa , likitoci da nas-nas suna aiki cikin awoyi 24 . Ba su ji tsoron gajiya da wahala ba , amma abin da ya fi ban tsoro shi ne ciwon sida ya kawo musu barazana . Mr. Sun ya ce , a cikin mutanen da suke kwana a cikin asibitoci , kashi 72 cikin 100 masu fama da ciwon sida ne . Kuma sharadin rigakafinmu ba shi da kyau .

A wata ranar Watan Satumba , wani sojan kasar Habasha ya zo ganin likita . Daga bisani an tabbatar da cewa , ciwon kanjamau ya harbe shi , kuma shi ne mai ciwon huhu mai tsanani . Da ya shiga cikin asibitin , nan da nan ya tufa da majina tare da jini har zuwa zanen gado da fararin tufafin nas nas . Ko da ya ke yana kasance da hadari , amma duk da haka sojoji da likitoci da nas nas na kasar Sin suna mai da hankali kwarai da gaske kan warkar da shi . Daga karshe dai halin ciwon wannan soja ya sassauta .

A watan Disamba na wannan shekara , wadannan sojojin kasar Sin za su gama aikinsu na watanni 8 a Afrika , amma ko shakka babu aikin da suka yi a kasar Liberia zai zama abin tunawa har abada .

To, jama'a masu sauraro , shirin "Duniya ina labari " game da sojojin kasar Sin suna kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Lawal Mamuda ne ya karanto muku . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri . (Ado)


1  2