Wakilin Rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa , A watan Afrilu na wannan shekara , kasar Liberia wadda take cikin farfadowa ta yi karbuwar sojoji masu kiyaye zaman lafiya na karo na 4 na kasar Sin . Sojojin suna kunshe da masu lalata nukiyoyi da masu jiyya da masu jigilar kayayyki . Yanzu watanni fiye da 6 sun shige , wakili Rediyon kasar Sin dake kasar Nijeriya ya kai ziyara ga wadannan sojojin kasar Sin dake kasar Liberia .
Yaran wata makarantar firamare dake wani gari na arewa maso gabashin kasar Liberia suna son sojojin kasar Sin kwarai da gaske . Shugaban Makarantar Mr. Henry ya gaya wa wakilin Rediyonmu cewa , sojojin kasar Sin sun baje wani tudun wada , sa'an nan kuma hanya ta yi lebur kuma fili ya yi lebur . Mr. Henry ya ce , wannan yana da muhimmanci sosai , saboda nan gaba kadan za a gina wata makarantar firamare . Yaran wannan makarantar sun ce sojojin kasar Sin suna da kirki , Sinawa suna da kirki .
1 2
|