

Mr. Dzoro ya kuma yi wa gwamnatin kasar Sin godiya da babban yabo saboda har kullun tana sa kaimi da kuma goyon bayan jama'arta da su yi yawon shakatawa a kasashen Afirka. Ya kara da cewa, jama'ar Sin masu jaraba abokai ne na jama'ar Kenya. Saboda bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen Kenya da Sin lami lafiya, yawan masu yawon shakatawa na kasar Sin da suka zo kasar Kenya ziyara zai karu a ko wace shekara. Ya ce,(murya ta 5, Dzoro)
'Ina fatan masu yawon shakatawa na kasar Sin za su gane cewa, kasar Kenya tana maraba da su, kuma kai wa kasar Kenya ziyara koma gida ne a gare su.' 1 2 3
|