Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 17:42:16    
Yanayi da zaman fararren hula na jihar Guangxi sun samu kyautatuwa sosai sakamakon yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki

cri

Raya da kuma yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki ta ba da tasiri a wasu fannoni a wurin. Jiang Ruohai, mataimakin shugaban hukumar kula da gundun daji ta birnin Guilin na jihar Guangxi ya bayyana cewa, "Ana daukar yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki da kuma dabarun yin amfani da makamashi tamkar wani irin juyin juya hali ne da aka yi a tarihin bunkasuwar makamashi a kauyuka. Ba kawai ana iya saukaka manoma daga ayyukansu masu dimbin yawa ba, har ma yawan gundun daji da ke birnin Guilin ya karu daga kashi 37.7 cikin dari a shekara ta 1980 zuwa 66.46 cikin dari na yanzu."

Manoman jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai sun samu alheri sosai sakamakon nasarar da jihar ta samu a fannin yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki. Bugu da kari kuma an samu wata sabuwar hanyar raya kauyuka ta yin amfani da iskar. Mutane masu yawa daga kasashen waje sun je jihar domin yin bincike da kuma koyi da sakamako mai kyau. Sabo da aka mayar da jihar Guangxi a matsayin wani muhimmin abin koyi na kasar Sin wajen koyi sakamakon mai kyau da ta samu wajen yaki da talauci, kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa da yawa sun zo jihar domin yin bincike. Dukkansu sun nuna sha'awa sosai ga yadda ake rayawa da yin amfani da iskar gas da aka samu daga taki. Game da wannan batu, Li Fangzhen, mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin amfani da kudaden kasashen waje a fannin yaki da talauci ta jihar Guangxi ya gaya wa wakilinmu cewa, "A ganina, yanayin kasashen Afirka ya yi zafi a gwargwado, wanda ya yi kama da yanayi na jihar Guangxi, shi ya sa suna da sharadin kafa wuraren samar da iskar gas da ake samu daga taki. 'yan Afirka da ke ziyarce mu sun nuna sha'awar sosai ga iskar, har ma suna son jaraba yadda ake yin amfani da wannan iskar gas da kansu a wuraren samar da iskar." (Kande Gao)


1  2  3